Fiye da jarirai 100 ‘yan bakwaini na cikin haɗari, bayan Isra’ila ta yanke wa Gaza man fetur — MƊD

Jarirai ‘yan bakwaini da marasa lafiya da ke ƙarƙashin kulawar gaggawa da masu ciwon ƙoda rayuwansu tana cikin haɗari bayan babbar tashar wutar lantarki ɗaya tilo a Gaza ta tsaya da aiki bayan da Isra’ila ta hana shigo da makamashi cikin Gaza.

Rayuwar jarirai aƙalla 120 da suke cikin kwalba a asibitoci a Gaza na cikin haɗari bayan da man fetur ya fara ƙarewa a yankin da aka yi wa ƙawanya, kamar yadda hukumar yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi.

Isra’ila ta kashe yara fiye da 1,750 kawo yanzu sanadin hare-hare ta sama da take kai wa Gaza a matsayin martani ga harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba, kamar yadda Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinawa ta bayyana.

Asibitoci suna fuskantar matsanancin ƙarancin magunguna da man fetur da ruwa ba kawai don kulawa da dubban mutane da suka jikkata ba hatta mutanen da ke neman kulawa ta yau da kullum a fiye da tsawon mako biyu na hare-haren da Isra’ila take kai wa a Gaza.

KU KUMA KARANTA: Ana tsananin buƙatar man fetur a Gaza, saboda ayyukan asibitoci — MƊD

“Yanzu haka muna da jarirai 120 waɗanda suke cikin kwalba, a cikinsu muna da guda 70 da ke kan na’urar janyo numfashi, shakka babu wannan ne babban abin damuwa,” in ji mai magana da yawun Asusun Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya Jonathan Crickx a ranar Lahadi.

Matsalar wutar lantarki tana daga cikin manyan abubuwan damuwa ga asibitocin ƙwararru bakwai a faɗin Gaza da ke kula da jarirai bakwaini ta fuskar taimaka musu wajen numfashi da sauran kulawa, misali idan wasu sassan jikinsu ba su gama girma ba.

Ƙarancin man fetur ya jawo cikas ga ayyukan agaji.

Isra’ila ta bayar da umarnin mamaye gaba ɗaya Gaza bayan Hamas ta kai mata hare-hare, inda ƙungiyar ta kashe mutum 1,400 kamar yadda mahukunta a Isra’ila suka bayyana.

Yayin da ake ci gaba da fuskantar yankewar wutar lantarki, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a ranar Alhamis ta yi gargaɗin cewa man fetur ɗin injinan janareton asibitoci ya fara ƙarewa.

Hukumar WHO ta ce kimanin mutum 1,000 da ke buƙatar wankin ƙoda za su faɗa haɗari idan injinan janareton suka daina aiki.

Manyan motoci ɗauke da kayan agaji guda 20 ne suka shiga Gaza daga Masar a ranar Asabar, sai dai babu man fetur a cikin kayayyakin.

Isra’ila tana jin tsoron cewa man fetur zai iya taimaka wa Hamas, kodayake akwai ragowa a Gaza wanda ake amfani da shi a injinan janareto don na’urorin kiwon lafiya su ci gaba da aiki.

“Idan aka sa su (jarirai) a kan na’urar taimaka wa mutum numfashi, haka yana nufin, idan wuta ta yanke, dole mu damu game da rayuwarsu,” in ji mai magana da yawun Hukumar UNICEF kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

A ranar Asabar Ma’aikatar Kiwon Lafiya a Gaza ta ce jarirai bakwaini 130 na haɗarin mutuwa saboda ƙarancin man fetur.

Mata kimanin 160 ne suke haihuwa a kowace rana a Gaza, kamar yadda hukumar da ke kula da yawan jama’a ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, wacce ta yi ƙiyasin akwai mata masu ciki 50,000 a yankin mai ƙunshe da mutum miliyan 2.4.

Yayin da Isra’ila take kai hari ga Hamas, wacce ta kai munanan hare-hare kan Isra’ila a tarihi tun bayan kafa ta a shekarar 1948, yara ne adadinsu ya fi yawa a cikin jimullar mutum 4,385 da aka kashe da ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta ruwaito.

Gaba ɗaya iyali, ciki har da mata masu ciki, an kashe su a hari ta sama kuma a kowace rana iyaye suna ganin ta’asar da ake yi, gawawwakin jarirai a cikin likkafani a kan tituna.

Likitoci a asibitin Najjar Hospital a Rafah sun yi magana a ranar Alhamis yadda suka yi ƙoƙarin ceto wani jarirai da ke cikin mahaifiyarsa wacce aka kashe a wani hari ta sama yayin da take zaune a gida.

Sa’o’in da suka gabata, yara takwas aka kashe yayin da suke bacci a gida a garin Khan Younis a kudancin Gaza.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *