Fitacciyar mawaƙiya Onyeka Onwenu, ta rasu

0
56
Fitacciyar mawakiya, Onyeka Onwenu, ta rasu

Fitacciyar mawaƙiya Onyeka Onwenu, ta rasu

Fitacciyar mawaƙiyar nan ‘yar Najeriya Onyeka Onwenu ta rasu a asibitin Reddington da ke Legas bayan da ta yanke jiki ta faɗi a wajen wani bukin murnar zagayowar shekarar haihuwa.

Rahotanni na nuni da cewa, marigayiyar ta gama waƙa a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar Misis Stella Okoli, ta je ta zauna ke nan sai ta yanke jiki ta faɗi daga nan aka garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar rai ya yi halinsa.

An haife Onyeka Onwenu ne ranar 31 ga Janairu 1952. Ita ce ƙaramar ɗiyar masanin ilmin Najeriya kuma ɗan siyasa D. K. Onwenu, wanda ya rasu tana da shekaru huɗu da haihuwa, mako guda kafin a naɗa shi a matsayin Ministan Ilimi.

Onyeka Onwenu ta yi makaranta a ciki da wajen Najeriya. Ta yi karatu a fanin hulɗa da jama’a da sadarwa a wata Jami’ar Amurka dake jihar Massachusetts, da kuma yi karatu a fannin nazarin zamantakewa a wata jami’ar dake birnin New York.

KU KUMA KARANTA: Babban sakatare na jami’ar Gurguzu a Vietnam, Nguyen Phu Trong, ya rasu

Marigayiyar tayi aiki a tashar talabijin ta kasa NTA inda ta gabatar da shirye shirye da suka yi fice da dama. Ta kuma zama member kwamitin darektocin tashar ta NTA.

Onyeka Onwenu ta fara waƙe-waƙe a shekarar 1981 lokacin tana aiki da NTA, daga baya ta koma yin wakokin bishara a cikin shekara ta 1990, Ta ci gaba da yin rubuce-rubuce da waƙoƙi kan batutuwan da suka shafi kiwon lafiya (HIV/AIDS), zaman lafiya, da zaman tare, mutunta ’yancin mata, da halin da yara ke ciki. Tana kuma wallafa shawarwari ga mata a dandalin sada zumunta na X.

Marigayiyar ta kuma yi fice a fannin wasannin fina-finai da ake nunawa a gidajen talabijin a wancan lokacin.

Onwenu ta kuma shiga siyasa ta tsaya takara ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP.

Ta yi takarar zama shugabar ƙaramar hukumarta Ideato ta Arewa a jihar Imo har sau biyu amma bata sami nasara ba.

Daga baya, tsohon gwamnan jihar Imo Ikedi Ohakim ya naɗa ta Shugabar Majalisar Fasaha da Al’adu ta Jihar Imo.

A ranar 16 ga Satumba, 2013, Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya nada ta Babbar Darakta, kuma Babban Jami’ar Cibiyar Bunkasa Rayuwar Mata ta Ƙasa.

Onyeka Onwenu ta rasu tana da shekaru 73 a duniya, ta bar ‘ya’ya maza biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here