Fetur Na Kowane Dan Najeriya Ne Ba ‘Yan Naija Delta Ba – Obasanjo

0
330

Obasanjo ya ce APC da PDP sun gaza

Daga Rabo Haladu

Obasanjo ya ce Najeriya dunkulalliyar kasace da babu wanda ya isa ya raba ta

Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce man fetur da ma sauran albarkatun kasar na dukkan ‘yan Najeriya ne.

Ya bayyana haka ne a wani martani da ya mayar wa fitaccen dattijon nan na yankin Naija Delta, Cif Edwin Clark, wanda ya zargi Obasanjo da nuna halin ko-in-kula game da illolin da hakar mai a yankin nasu ta haddasa.

Wasu rahotanni sun ambato Clark, a cikin wata wasika da ya rubuta, yana zargin tsohon shugaban kasar da nuna kiyayya ga masu fafutukar mallakar albarkatun kasar da aka samu a yankunansu

Sai dai a martanin da ya mayar, Obasanjo ya ce a iya saninsa albarkatun kasar da aka hako a Najeriya mallakin dukkan ‘yan kasar ne ba na mutanen yankunan da aka same su ba.Ya kara da cewa ba zai yiwu a samu kasashe biyu a cikin kasa daya ba, yana mai cewa a iya fahimtarsa Cif Clark yana magana ne a kan samar da wata kasa a cikin Najeriya idan har yana so a ba Naija Delta damar mallakar albarkatun kasar da aka samu a yankin.

A cewarsa, kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya yarda cewa zinaren da aka samu a Zamfara, ko “zinaren da aka samu a Ilesha da ke Jihar Osun, da kuma ma’adinin lead da ke Jihar Ebonyi” shi ne kuma ya bayyana cewa fetur din da aka samu a Naija Delta duka na ‘yan kasar ne.

Tsohon shugaban kasa ya ce dukkan mutanen da suka kulla yarjejeniyar sayen danyen man fetur sun yi ne da Najeriya a matsayin kasa ba da yankin Naija Delta ba, yana mai jaddada cewa Najeriya dunkulalliyar kasa ce da babu wanda ya isa ya raba ta, ciki har da raba albarkatun da ke cikinta.

A cewarsa: “Idan akwai wata barazanar tsaro a kowanne bangare na Najeriya a yau, ciki har da yankin Naija Delta, sojojin Najeriya ne tare da tallafin wasu jami’an tsaro, a matakin gwamnatin tarayya, za su yi raddi kan hakan.”

Masu fafutuka a yankin Naija Delta sun dade suna kokarin ganin sun mallaki fetur din da ake hakowa a yankinsu, inda a wasu lokutan lamarin yakan kai ga kashe-kashe da satar ma’aikatan man fetur


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here