Fastoci sun ziyarci waɗanda harin bom ɗin Mauludi ya shafa a Asibiti

0
213

Fastoci sun kai ziyara domin jajanta wa waɗanda iftila’in harin bam ɗin jirgin soji ya shafa a asibitin Barau Dikko inda suke karɓar magani.

Jagoran masu ziyarar, Fasto Yohanna Buru, ya ce, makasudin ziyarar shi ne domin yi wa marasa lafiyar addu’ar samun sauki tare kuma da jajantawa.

Aminiya ta ruwaito cewa harin bam ɗin a ƙauyan Tudun Biri a ƙaramar hukumar Igabi ya tayar da hankalin mutanen ƙasar nan matuka.

Aƙalla mutum 100 ake ganin sun rasu bayan wani jirgin soja maras matuki ya sakar masu bam har sau biyu a wurin Taron Maulidi.

KU KUMA KARANTA: Sheikh Muhajjadina ya yi Allah wadai da harin sojoji kan masu Mauludi a Kaduna

Fasto Buru ya yi addu’ar Allah Ya jikan waɗanda suka rasu Ya kuma sa mutuwar shahada suka yi.

Ya kuma buƙaci gwamnati da ta yi dukkan mai yiwuwa wurin tallafa wa waɗanda abin ya shafa domin rage masu raɗaɗi.

Shi ma da yake jawabi a wurin, Fasto George John cewa ya yi dalilin ziyarar shi ne domin yi wa marasa lafiyar addu’a tare da fatan samun sauki cikin hanzari.

Leave a Reply