Farashin man fetur na iya tashi bayan Ɗangote ya dakatar da sayar da ɗanyen-mai da Naira
An fara nuna fargabar yiwuwar ƙarin farashin litar man fetur a kasarnN, bayan rahoton cewa kamfanin Dangote ya dakatar da sayar da man ga ‘yan kasuwa ta hanyar biyan kuɗi da naira.
Kamfanin ya sanar da ‘yan kasuwa a ranar Juma’a cewa wannan mataki zai fara aiki daga Lahadi, 28 ga Satumba, 2025, bayan ya ce ya kammala amfani da rabon danyen mai da aka ware masa a ƙarƙashin tsarin “Crude-for-Naira”.
KU KUMA KARANTAMatatar Ɗangote ta fitar da motoci 1,000 don fara rarraba man fetur kai tsaye ga jihohin Najeriya
Sanarwar, wacce sashen kasuwanci na matatar Dangote ya sanya wa hannu, mai taken: “Dakatar da Sayar da man fetur da Naira – daga 28 ga Satumba, 2025.”
Kamfanin ya kuma umarci kwastomomi da ke da cinikayyar da suka dogara da biyan kuɗi a naira da su nema a maido musu da kuɗinsu.









