Faransa ta soke ƙudirin mika ƙanin tsohon shugaban Burkina Faso Blaise Compaire ga kotun ƙasar

0
118

Faransa ta soke wani ƙudirin ministan shara’ar ƙasar na 2020, da ya buƙaci tisa keyar François Compaoré, ƙanin tsohon shugaban ƙasar Burkina Faso  Blaise Compaoré, a ƙasarsa, domin fuskantar shara’ar tuhumar aikata kisan shahararen ɗan jaridar nan Norbet Zongo, da wasu abokan tafiyarsa 3 a ranar 13 disamba 1998.

Ƙuduri da ya soke aniyar an tabbatar da shi ne tun ranar 13 ga watan desemba wannan shekara ta 2023, amma sai a ranar 20 ga watan na disamba ne, shugaban babban ɗakin shara’ar tisa keyar masu laifi, na babbar kotun birnin paris ya sanar a lokacin shara’ar, da ta bukaci soke ƙudirin tisa ƙeyar ta François Compaoré, a Burkina Faso domin fuskantar shara’a da aka ƙudiri aniyar yi a 2017.

Leave a Reply