Faransa na shirin rufe ofishin jakadancinta da ke Jamhuriyar Nijar, inda ake ci gaba da nuna mata tsangwama tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin da ya gabata.
Matakin rufe ofishin jakadancin na zuwa ne bayan ɗimbim ma’aikatan diflomasiyar Faransa sun fice daga ƙasar sakamakon hare-hare, abin da ya sa ofishin ya dakatar da aikace-aikacensa kamar yadda majiyoyin diflomasiyya suka bayyana.
Majiyoyin sun ce, bayan wani hari da aka kaddamar kan ofishin jakadancin a ranar 30 ga watan Yuli da kuma yadda sojojin kasar suka toshe hanyoyin da ke kewayen harabar ginin ofishin, akasarin ma’aikatan diflomasiyyar sun fice daga ƙasar a ƙarshen watan Satumba.
Wannan al’amari ne ya hana ofishin jakadancin ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda ya saba, abin da ya sa gwamnatin Faransa ta yanke shawarar rufe ofishin jakadancin.
Tuni aka sallami ma’aikata ‘yan asalin Nijar da ke aiki a ofishin jakadancin bayan an yi musu ihsani kamar yadda majiyoyin na diflomasiyya suka tabbatar.
KU KUMA KARANTA: Rukunin ƙarshe na sojojin Faransa na kammala ficewa daga Nijar
Danganta tsakanin Nijar da Faransa ta yi tsamin bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yuli, inda suka kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum.
Sojojin da suka ƙwace mulkin sun soke yarjeniyoyin tsaro da Faransa, yayin da suka kori jakadan ƙasar, inda kuma suka ƙulla alaƙar kut da kut da Rasha.