Falasɗinawa sun koma binne iyalansu a gefen titi da asibitoci da filayen makarantu

0
250

Falasɗinawa da dama na binne iyalansu da suka rasu sakamakon hare-haren sojojin Isra’ila a gefen titi da asibitoci da wuraren wasan yara.

Hakan ya faru ne sakamakon irin wahalar da Falasɗinawan ke sha kafin zuwa makabartu domin binne ‘yan uwansu.

Falasɗinawan da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya tattauna da su sun shaida cewa kabururan za su kasance na wucin gadi har zuwa lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, inda suka ce idan an samu hakan sai su mayar da gawarwakin zuwa makabartu.

KU KUMA KARANTA: An kashe Falasɗinawa 100 a hare-haren da aka kai musu cikin dare a Gaza

Shugaban ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Euro-Mediterranean Observatory for Human Rights, Rami Abdu ya bayyana cewa jami’ansa sun gano kaburbura na gefen titi sama da 120 waɗanda aka binne mutane da dama a ciki.

Leave a Reply