Connect with us

Ƙasashen Waje

Falasɗinu ta buƙaci Isra’ila ta biya kuɗin sake gina Gaza

Published

on

Hukumomin Falasɗinu sun buƙaci Isra’ila ta ɗauki nauyin biyan kuɗin sake gina Gaza da kuma nuna babbar himma wajen tabbatar da sulhu tsakanin ƙasashen biyu.

Firaiminista Muhammad Shtayyeh ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da Ministan Harkokin Wajen Japan Tsuji Kiyoto a birnin Ramallah, inda ya ce: “Dole ne a ɗora wa Isra’ila alhakin ɓarnar da aka yi a Zirin Gaza da kuma ɗaukar nauyin sake gina ta.”

Gwamnatin Shtayyeh za ta yi aiki a matsayin gwamnatin riƙon ƙwarya har sai an kafa sabuwar gwamnati, bayan da ya yi murabus a ranar Litinin.

Shtayyeh ya kuma yi Allah wadai da matakin na Isra’ila, yana mai cewa “tana aiwatar da mummunan zalunci kan al’ummar Falasɗinu, tana ƙarfafa wariyar launin fata da kuma nuna kamar ba za ta fuskanci wani sakamako na shari’a ba.”

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 3 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba da ta’azzara

Ya jaddada cewa, babban abin da ya sa a gaba shi ne dakatar da kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummarmu a Zirin Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan, ciki har da Birnin Ƙudus, da kuma ƙara buɗe mashigar Zirin Gaza domin ba da damar taimakon jinƙai da na lafiya cikin gaggawa.

Shtayyeh ya kuma bayar da shawarar “ƙara yin ƙoƙarin kiyaye hanyar samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu da aiwatar da ƙudurin cimma hakan ta hanyar kawo ƙarshen mamayar da kuma amincewa da ƙasar Falasɗinu kamar yadda yake a cikin dokokin 1967 da sany Ƙudus a matsayin babban birninta.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

‘Yan sandan Kenya 400 sun tafi Haiti don aikin wanzar da zaman lafiya

Published

on

'Yan sandan Kenya 400 sun tafi Haiti don aikin wanzar da zaman lafiya

‘Yan sandan Kenya 400 sun tafi Haiti don aikin wanzar da zaman lafiya

Wata tawagar ‘yan sandan Kenya 400 ta tashi daga birnin Nairobi ranar Talatar nan zuwa ƙasar Haiti don aikin wanzar da tsaro.

‘Yan sandan, waɗanda za su jagoranci jami’an tsaro kimanin 1,000 na Majalisar Ɗinkin Duniya, za su fafata da gungu-gungu na masu aikata laifuka a Haiti domin maido da zaman lafiya a ƙasar.

“Muna alfaharin ganin tashin rukunin farko na ‘Yan Sandan Ƙasarmu waɗanda za su kasance a tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya don aikin waznar da tsaro a Haiti,” a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Kenya Kithure Kindiki, a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ƙara da cewa manyan jami’an ‘yan sanda na ƙasar Kenya da kuma jami’ai daga ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ne suka halarci bikin tashin ‘yan sandan zuwa ƙasar da ke yankin Caribbea.

KU KUMA KARANTA: Kenya ta soma sauraron ƙararraki kan zargin cin zarafi da sojojin Birtaniya suka yi

Tawagar ta ƙunshi zaratan ‘yan sanda na rundunoni na musamman na Kenya waɗanda suka haɗa da Sashen Kai Ɗaukin Gaggawa da Sashen Gudanarwa da kuma ‘yan sandan gama-gari.

A yayin da yake jawabi gabanin tura ‘yan sandan a Kwalejin Horas da ‘yan sanda da ke Embakasi, Shugaban Kenya William Ruto ya ce, “Kenya tana da tarihin jajircewa a aikin wanzar da zaman lafiya da magance rikici a duniya.
Zuwan ‘yan sandanmu Haiti zai kawo sauƙi ga rayuwar maza da mata da yara da suka tagayyara sakamakon rikicin ‘yan bindiga.”

Ya ƙara da cewa, “Za mu yi aiki da ƙasashen duniya domin maido da zaman lafiya mai ɗorewa a Haiti.”

Haiti ta kwashe shekaru da dama tana fama da rikicin ‘yan bindiga. Lamarin ya yi ƙamari a watanni baya bayan nan, inda ‘yan bindiga suka riƙa sace mutane da kashe su da aikata migayun ayyuka.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Sojojin Amurka na neman wani sansanin a Yammacin Afirka bayan korar su da Nijar ta yi

Published

on

Sojojin Amurka na neman wani sansanin a Yammacin Afirka bayan korar su da Nijar ta yi

Sojojin Amurka na neman wani sansanin a Yammacin Afirka bayan korar su da Nijar ta yi

Janar C.Q. Brown, Hafsan Sojin Sama na Amurka kuma shugaban Hafsoshin Sojin Amurka, wanda ke tafiya zuwa taron hafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka, ya faɗa wa ‘yan rahoto gabanin saukar jirginsa a Botswana ranar Litinin cewa, zai zanta da abokan aiki daban-daban a yankin.

Janar Brown ya faɗa wa ‘yan jaridar da ke tafiya tare da shi cewa, “Ina ga akwai wasu damarmaki. Kuma akwai ƙasashen da tuni muna aiki tare da su a Afirka ta Yamma”.

Ya ƙara da cewa gina wannan dangantaka za ta iya “samar da damarmaki gare mu don haɓaka ƙarfin da muke da shi a baya a Nijar da sauran wurare”.

Amma Janar Brown ya ƙi ya faɗi waɗanne ƙasashen ne Amurka take dubawa. Amma wani jami’in Amurka ya gaya wa Reuters cewa gwamnatin Shugaba Joe Biden ta fara tattaunawa da ƙasashe kamar Benin da Ivory Coast da Ghana.

Sai dai ba a tunanin sojin Amurka za su iya miƙe ƙafa wajen maimaita abin da suka yi a Nijar don yaƙi da ta’addanci a nan kusa.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Amurka za su kammala ficewa daga Nijar 15 ga Satumba

Abin lura shi ne, korar da aka musu a Nijar na nufin sun yi asarar filin jirgi na 201, wanda Amurka ta gina a kusa da Agadez da ke tsakiyar Nijar, wanda ta kashe dala miliyan 100.

Kafin juyin mulkin sojin Nijar na bara, sansanin sojin ya kasance jigo ga yaƙin da Amurka da Nijar suke yi kan ‘yan ta’adda da suka kashe dubban mutane, kuma suka tagayyara ƙarin miliyoyi.

Wani jami’in Amurka daban, shi ma ya faɗa cikin sirri cewa, ba a saka ran ganin wani babban sansanin sojin Amurka, ko kuma yin ƙaura gaba ɗayan rundunar daga Nijar zuwa wani wuri.
Jami’in na biyu ya ce, “Ba ma sa ran jin sanarwar wani babban aikin gina sansanin soji a ko ina nan kusa”.

Yanayin siyasa mai cike da ƙalubale a Yammaci da Tsakiyar Afirka yana da sarƙaƙiya ga Amurka. Yankin ya fuskanci juyin mulkin soji har guda takwas cikin shekaru huɗu, ciki har da na Nijar da maƙwabtanta Burkina Faso da Mali.

Gwamnatocin sojin da ke mulkin yawancin ƙasashen sun ja baya da aiki tare da ƙasashen Yamma har da Amurka, – wadda a doka ta haramta wa sojinta taimaka wa gwamnatocin da suka ƙwace mulki ta juyin mulki. Ƙasashen suna ci gaba da komawa wajen Rasha, wadda ba ta da irin wannan tarnaƙin.

“Amurka ta daɗe tana da abokan aiki a yankin,” cewar Catherine Nzuki wadda ke cibiyar Center for Strategic and International Studies da ke Washington.

“Kuma yanzu da aka kori Amurka daga Nijar, babbar tambayar da Ma’aikatar harkokin Waje, da Ma’aikatar Tsaron Amurka ke yi ita ce: Shin muna rasa abokai ne a yankin? Shin abubuwa na sauyawa cikin hanzarin da muka kasa bibiyar su?”

Jami’in Amurka na biyun ya amsa cewa sojin Amurka suna nazarin sauye-sauyen da ke faruwa cikin gaggawa.

“Muna nazari cikin tsanaki a yanzu kuma muna tunani game da yadda manufofinmu za su kasance,” cewar jami’in.

Ƙarfin da Amurka za ta samu tare da sabbin manufofin, wajen samun damar daƙile barazanar ƙungiyoyin masu amfani Musulunci suna faɗaɗa a yankin Sahel mai fama da matsanacin yanayin muhalli da arziƙi, wanda har yanzu ba a fayyace ba.
“Barazanar ‘yan ta’adda ta yi ƙamari,” cewar jami’in na biyu.

Zuwa yanzu, janyewar Amurka daga Nijar tana kammala kamar yadda aka tsara gabanin wa’adin 15 ga Satumba, jami’an Amurka sun ce, da rundunar da ba ta wuce 600 ba da ta rage a sansanin Air Base 101, abin da ya rage shi ne tafiya filin jirgin sama na Diori Hamani International Airport, da ke Niamey.

Yayin da Amurka ke ficewa, Rasha ta girke tarin jami’an soji a wannan sansanin, inda suke gudanar da ayyukan ba da horo. Jami’an Amurka sun ce sojojinta ba sa wata mu’amala da takwarorinsu na Rasha.

Janar Brown ya bayyana fatan cewa ko da bayan ficewar Amurka, za a iya samun hanyar ci gaba da alaƙar tsaro a gaba, tare da Nijar, ganin tsawon shekarun da aka yi ana zuba kuɗi da ƙulla alaƙar soji.

“Muna da ofishin jakadanci a can, don haka muna da alaƙa har yanzu. Don haka ban san ko ƙofar ta kulle gabaɗaya ba,” cewar Janar Brown. “Kenan a gaba, idan dama ta samu don sake gina alaƙa, da ƙarfafa dangantaka, za mu yi aiki da gwamnatin Amurka don gano hanyar da ta fi dacewa don yin haka.”

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Wani harin haɗin-gwiwa na Amurka da Birtaniya ya kashe mutum biyu a Yemen

Published

on

Wani harin haɗin-gwiwa na Amurka da Birtaniya ya kashe mutum biyu a Yemen

Wani harin haɗin-gwiwa na Amurka da Birtaniya ya kashe mutum biyu a Yemen

Sojojin Amurka da na Birtaniya sun sanar cewa sun kai hare-hare kan mayaƙan Houthi da ke Yemen.

Ranar Alhamis kafar watsa labarai ta Houthi ta tabbatar da kisan aƙalla mutum biyu a hare-haren.

Ma’aikatar tsaron Birtaniya ta ce an kai hare-haren na haɗin-gwiwa ne a wurare uku a birnin Hodeidah da ke gaɓar Bahar Maliya.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Amurka za su kammala ficewa daga Nijar 15 ga Satumba

Gidan talbijin na Al Masirah wanda ƙungiyar Houthi take gudanar da shi ya ruwaito cewa an kashe aƙalla mutum biyu sannan aka jikkata mutum 10 a hare-haren da aka kai a wani gini na gidan rediyo a lardin Al-Hawk na birnin Hodeidah.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like