Falasɗinawa na cin abincin dabbobi saboda yadda yaƙin Isra’ila ya jawo yunwa a Gaza

0
121

Yayin da halin da Falasɗinawan ke ciki a Gaza ke ƙara ta’azzara a kowace rana a ƙarƙashin munanan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa, maudu’in #GazaStarving na ci gaba da yaɗuwa a shafukan sada zumunta inda aka nuna bidiyon da ke nuna mutane masu fama da yunwa suna cin abincin dabbobi, yayin da su kuma dabbobin suke cin gawarwakin mutane da ke yashe a kan tituna.

A cikin ‘yan kwanaki kaɗan kawai, an yi amfani da maudu’in #GazaStarving – sau kusan miliyan biyar a shafin X, yayin da a sauran shafukan sada zumunta, ciki har da Instagram da TikTok, ake amfani da maudu’in don bayyana yunwar da Falasɗinawa ke fuskanta.

Tashen da maudu’in #GazaStarving ke yi ya fito da ainihin fargabar yunwa da ake fama da ita a Gaza, yayin da rahotanni suka fara bayyana a shafukan sada zumunta na yadda Falasɗinawa ke niƙa abincin dabbobi saboda ƙarancin alkama da burodi.

Bidiyo da dama sun nuna Falasɗinawa da ke fama da yunwa suna cin abincin dabbobi, yayin da kyanwowi da karnuka suka mayar da gawarwakin mutanen da ke yashe a kan titi abincinsu.

Sojojin Isra’ila na ci gaba da aiwatar da munanan ayyukan da suke yi, tare da nuna ƙyama ga gawarwakin Falasɗinawan da ba a binne ba a kudancin birnin Khan Younis, tare da hana jama’a tattara su daga ɓaraguzan gine-gine, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa Anadolu a ranar Laraba.

KU KUMA KARANTA: Ya zama dole a amince da haƙƙin Falasɗinawa na kafa ƙasarsu – Majalisar Ɗinkin Duniya

Shaidun gani da ido sun ce wasu Falasɗinawa sun koma yankunan da sojojin Isra’ila suka janye domin gano gawarwakin ‘yan’uwansu da suka haɗa da yara da mata, waɗanda tankokin yakin Isra’ila suka kai musu hari a yayin da suke yunƙurin tserewa daga birnin Khan Younis zuwa Rafah mai nisa daga.

Sun ce motocin ɗaukar marasa lafiya sun yi jigilar wasu gawarwakin zuwa cibiyar kula da lafiya ta Nasser da ke tsakiyar birnin, amma lokacin da tankunan Isra’ila suka buɗe wuta kan kowa da kowa a yankin, sai da jami’an agajin suka gudu.

Wasu daga cikin gawarwakin sun fara ruɓewa, kuma wasu kyanwowi da karnuka sun cinye sassan jikinsu, in ji su.

Hotunan bidiyo da dama da suka yi amfani da maudu’in sun nuna Falasɗinawa suna cin biredin da aka yi da abincin dabbobi.

A cewar wani wakilin Anadolu a arewacin Gaza, an lura cewa mutane suna sayen abincin dabbobi a kasuwannin arewacin Gaza a matsayin abincinsu, saboda yadda fulawa da alkama suka yi ƙaranci.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa mutum miliyan 2.2 a Gaza, ƙarƙashin hare-haren Isra’ila, na fuskantar barazanar yunwa.

Yayin da Isra’ila ke barin wasu motocin agaji kaɗan zuwa Gaza, an kuma raba waɗannan manyan motocin ne a yankunan kudancin Gaza, yayin da ake ci gaba da hana yankunan arewacin Gaza saboda mamayar Isra’ila.

Isra’ila ta kai wani mummunan hari a Zirin Gaza bayan harin ba-zata da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 25,700 tare da jikkata 63,740. Kusan ‘yan Isra’ila 1,200 ne ake kyautata zaton an kashe a harin na Hamas.

Leave a Reply