Falasɗinawa na ɓuya a tsohon gidan yari saboda babu sauran mafaka a Gaza

0
38
Falasɗinawa na ɓuya a tsohon gidan yari saboda babu sauran mafaka a Gaza

Falasɗinawa na ɓuya a tsohon gidan yari saboda babu sauran mafaka a Gaza

Yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza, wanda ya shiga kwanaki 294, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,175, akasarinsu mata da yara, tare da jikkata mutum 90,403, kana an ƙiyasta cewa an binne fiye da mutum 10,000 a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.

Bayan da Isra’ila ta kwashe makonni tana kai musu hari babu inda za su je, ɗaruruwan Falasɗinawa sun koma ɓuya a wani tsohon gidan yarin Gaza da aka gina domin tsare masu laifin kisan kai da ɓarayi.

Yasmeen al-Dardasi ta ce ita da ‘yan’uwanta suna ji suna gani suka dinga wuce wasu mutanen da suka samu raunuka da ba za su iya taimaka musu ba yayin da suke ƙaura daga wasu yankuna da ke kudancin birnin Khan Younis zuwa gidan yarin.

Sun yini a ƙarƙashin bishiya kafin su wuce zuwa tsohon gidan yarin, inda yanzu suke zaune a ɗan ƙaramin masallacin da ke wajen. Suna samun kariya daga zafin rana, amma babu sauran jin daɗi.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 48 a Gaza a ƙasa da awa ɗaya

Mijin Dardasi yana fama da ciwon ƙodar da huhu, amma babu katifa ko bargo. “Mu ma ba mu zauna a nan ba,” in ji Dardasi, wadda kamar sauran Falasɗinawa tana fargabar yaƙi ya sake cim mata.