Falasɗinu ta buƙaci Isra’ila ta biya kuɗin sake gina Gaza

0
147

Hukumomin Falasɗinu sun buƙaci Isra’ila ta ɗauki nauyin biyan kuɗin sake gina Gaza da kuma nuna babbar himma wajen tabbatar da sulhu tsakanin ƙasashen biyu.

Firaiminista Muhammad Shtayyeh ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da Ministan Harkokin Wajen Japan Tsuji Kiyoto a birnin Ramallah, inda ya ce: “Dole ne a ɗora wa Isra’ila alhakin ɓarnar da aka yi a Zirin Gaza da kuma ɗaukar nauyin sake gina ta.”

Gwamnatin Shtayyeh za ta yi aiki a matsayin gwamnatin riƙon ƙwarya har sai an kafa sabuwar gwamnati, bayan da ya yi murabus a ranar Litinin.

Shtayyeh ya kuma yi Allah wadai da matakin na Isra’ila, yana mai cewa “tana aiwatar da mummunan zalunci kan al’ummar Falasɗinu, tana ƙarfafa wariyar launin fata da kuma nuna kamar ba za ta fuskanci wani sakamako na shari’a ba.”

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 3 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba da ta’azzara

Ya jaddada cewa, babban abin da ya sa a gaba shi ne dakatar da kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummarmu a Zirin Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan, ciki har da Birnin Ƙudus, da kuma ƙara buɗe mashigar Zirin Gaza domin ba da damar taimakon jinƙai da na lafiya cikin gaggawa.

Shtayyeh ya kuma bayar da shawarar “ƙara yin ƙoƙarin kiyaye hanyar samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu da aiwatar da ƙudurin cimma hakan ta hanyar kawo ƙarshen mamayar da kuma amincewa da ƙasar Falasɗinu kamar yadda yake a cikin dokokin 1967 da sany Ƙudus a matsayin babban birninta.”

Leave a Reply