Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata rahoton ‘Bankin Duniya’ kan talauci a Najeriya

0
196
Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata rahoton 'Bankin Duniya' kan talauci a Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata rahoton ‘Bankin Duniya’ kan talauci a Najeriya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya da ya ce mutane miliyan 139 a Najeriya na fama da talauci, tana mai cewa wannan adadi bai dace da ainihin halin tattalin arzikin ƙasar ba.

Kakakin Shugaba Tinubu, Sunday Dare, ya bayyana cewa ƙididdigar ta dogara ne da tsohon tsarin $2.15 a rana wanda idan aka juyar da shi da kudin Najeriya yanzu zai kai kusan N100,000 a wata, fiye da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya yafe wa Mamman Vatsa, Herbert Macaulay da wasu mutane 174

Gwamnati ta bayyana cewa rahoton ya ta’allaka ne da tsofaffin bayanai na 2018/2019 kuma bai la’akari da ɓangarorin tattalin arzikin da ba su cikin hukumance kamar kasuwanci da noma ba.

Ta ce rahoton kawai hasashe ne na duniya, ba ainihin halin da ake ciki ba, tare da jaddada cewa tattalin arzikin ƙasar na samun farfaɗowa da ci gaba ta hanyar manufofin gyara.

Fadar ta kuma bayyana shirye shiryen tallafi da gwamnati ke aiwatarwa don rage talauci, ciki har da tallafin kuɗi ga gidaje miliyan 15, shirye-shiryen N-Power da GEEP, ciyar da ɗalibai, da shirye-shiryen tsaron abinci. Haka kuma, asusun gine-gine da lamunin ƙananan kasuwanci suna taimakawa wajen ƙirƙirar ayyuka da inganta rayuwar jama’a.

Leave a Reply