Connect with us

Ƙasashen Waje

Faɗa da ruwan bama-bamai a birnin Gaza bayan ba da umarnin kwashe jama’a

Published

on

Faɗa da ruwan bama-bamai a birnin Gaza bayan ba da umarnin kwashe jama'a

Faɗa da ruwan bama-bamai a birnin Gaza bayan ba da umarnin kwashe jama’a

An gwabza ƙazamin faɗa da ruwan bama-bamai a birnin Gaza da wasu yankunan Falasɗinawa a yau Juma’a yayin da masu shiga tsakani ke ci gaba da kokarin dakatar da yakin da ya shiga cikin wata na goma.

Shugaban Amurka Joe Biden ya faɗa a taron Ƙungiyar Tsaro ta NATO a birnin Washington jiya Alhamis cewa jami’an diflomasiyyar Amurka, duk da matsalolin da ake fuskanta, suna samun “ci gaba” tare da masu shiga tsakani na ƙasa da ƙasa wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tare da jaddada cewa “lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen wannan yaƙi”.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 29 a harin da ta kai a wata makaranta a Gaza

Kafofin yaɗa labarai masu alaƙa da mahukuntan yankin Hamas, sun ce sojojin Isra’ila sun ƙaddamar da sabbin hare-haren sama fiye da 70.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoton mutuwar mutum 32, tana mai cewa “an kai waɗanda suka mutun, waɗanda akasarinsu yara da mata ne zuwa asibitoci cikin dare, saboda kisan kiyashin da ake ci gaba da yi”.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana kuma gwabza faɗa a yankin Rafah da ke kudancin ƙasar, inda dakarunta suka “kawar da ‘yan ta’adda da dama a hare-hare ta sama”.

Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Click to comment

Leave a Reply

Ƙasashen Waje

Isra’ila ta bai wa Falasɗinawan Gaza umarnin barin gidajensu – MƊD

Published

on

Isra'ila ta bai wa Falasɗinawan Gaza umarnin barin gidajensu - MƊD

Isra’ila ta bai wa Falasɗinawan Gaza umarnin barin gidajensu – MƊD

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana girman mamayar da sojojin Isra’ila suke yi wa yankin Gaza, tana mai cewa an kori kusan kashi 84 daga yankin.

Da yake bayani kan alƙaluman da Ofishin Babban Mai Kula da Harkokin Jinƙai na Majalisar (OCHA) ya tattara, mataimakin kakakin ofishin Farhan Haq ya shaida wa manema labarai cewa “luguden wuta da kuma kutsen da Isra’ila take yi a Gaza na ci gaba da kashewa da jikkatawa tare da korar Falasɗinawa daga matsugunansu, da kuma rusa gidajensu da sauran gine-gine da suka dogara a kansu.”

Ya ce, “Sau biyu sojoji suna bayar da umarni ga mutane su fita daga Khan Younis a ƙarshen mako, zuwa yankunan da a baya galibi aka umarci mutane su fice daga cikinsu.”

KU KUMA KARANTA: Dubban Falasɗinawa sun tsere daga wani yanki a tsakiyar Gaza

Wannan lamari ya shafi yankuna 23 da wurare 14 da ke samar da ruwa da tsaftar jama’a da kuma makarantu huɗu.

“Jimilla, sojojin Isra’ila sun kori mutane daga wurin da ya kai girman murabba’in kilomita 305, wato kusan kashi 84 na yankin Zirin Gaza,” in ji shi.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

DR Congo da Zambia sun fara tattaunawa game da rufe kan iyaka

Published

on

DR Congo da Zambia sun fara tattaunawa game da rufe kan iyaka

DR Congo da Zambia sun fara tattaunawa game da rufe kan iyaka

Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo ta ce ta fara tattaunawa da Zambia kwana guda bayan da maƙociyarta ta kudancin Afirka ta rufe iyakarsu.

Matakin ya toshe babbar hanyar da Congo ke amfani da ita don fitar da Copper zuwa ƙasashen waje, a matsayinta na ƙasa ta biyu a duniya a yawan fitar da ƙarfen Copper.

A ranar asabar, ministan kasuwanci na Zambia, Chipoka Mulenga ya sanar da rufe iyakar na wani ɗan lokaci, bayan Congo ta saka haramcin amfani da lemon zaƙi da barasa da aka shigo da ita, inda ya haifar da zanga-zangar direbobin dakon kaya a garin Kasumbalesa da ke iyakar Zambia.

KU KUMA KARANTA: Ukraine ta kai ƙazamin hari kan yankunan iyaka na Rasha

“An fara tattaunawa tsakanin gwamnatocin Congo da Zambia tun ranar Lahadin nan, don hanzarta sake buɗe ƙofar iyakar tasu,” in ji wata sanarwa da Ma’aikatar Kasuwanci ta Congo ta fitar a ranar Lahadi.

“A awannin da suka biyo baya, ɓangarorin biyu za su haɗu a Lubumbashi da ke Haut-Katanga, don nemo mafita ta ƙarshe game da kasuwancin.”

Ministan Kasuwanci na Congo, Julien Paluku Kahongya, ya fitar da sanarwa a ranar Lahadi, inda yake cewa ma’aikatarsa ta samu sanarwa a hukumance game da taƙaddamar kasuwanci daga Zambia kafin ta sanar da rufe iyakar.

A sanarwar, ya yi dogon bayani game da yarjejeniyar kasuwancin ƙasashen biyu da kuma hanyoyin magance duk wata taƙaddama da ta taso.

“Ya zuwa yanzu babu wata taƙaddama da aka gabatar wa ma’aikatar a rubuce, ko ta hanyar diflomasiyya,” in ji shi. “Ma’aikatar ta shirya duba duk wata buƙata da Zambia ta kawo, matuƙar tana ƙunshe cikin yarjejeniyar, wadda ta hana ramuwar gayya.”

Congo ce ƙasa ta biyu a duniya a fannin samar da ƙarfen Copper, kuma ta zo ta 3 a 2023 wajen fitar da shi, bayan ta fitar da tan miliyan 2.84.

Zambia hanya ce mai muhimmanci ga Congo, wajen fitar da Copper, inda ake bi ta garin Kasumbalesa a shiga Zambia.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

An soke wasannin da Taylor Swift za ta yi i a Austria

Published

on

An soke wasannin da Taylor Swift za ta yi i a Austria

An soke wasannin da Taylor Swift za ta yi i a Austria

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa da yawa daga cikin masoyan nata sun kashe dubban kuɗaɗen Euro wajen yin tafiya da kama otel da kuma abinci.

Masoyan Taylor Swift sun nuna rashin jin daɗinsu bayan da aka soke wasannin da mawaƙiyar za ta yi guda uku waɗanda tuni an kammala sayar da tikitinsu a Austria.

Soke wasannin ya biyo bayan bayanan sirri da hukumomin tsaro suka ce sun gano waɗanda ke cewa akwai a kai harin ta’addanci a birnin Vienna.

Da yawa daga cikin masoyanta sun ɗunguma zuwa shafukan sada zumunta don nuna rashin jin daɗinsu kan soke wasannin mawaƙiyar ta Amurka ‘yar asalin jihar Pennsylvania.

KU KUMA KARANTA;Ruwan sama ya lalata gidaje da dama a garin Faguji, jihar Bauchi

Wasu masoyan nata sun bayyana yadda suka kwashe watanni suna shirin halartar wasannin har ma suka ware wasu kaya na musamman da za su saka a lokacin.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa da yawa daga cikin masoyan nata sun kashe dubban kuɗaɗen Euro wajen yin tafiya da kama otel da kuma abinci.

Hukumomi sun ce sun kama mutum biyu masu tsatstsauran ra’ayi, inda ɗayansu ya amsa yin mubaya’a ga ƙungiyar IS mai iƙirarin jihadi.

Continue Reading

You May Like