Etsu Nupe ya naɗa sarakunan ƙauye 17, ya hore su akan zaman lafiya

A ranar Lahadin da ta gabata ne mai martaba Etsu Nupe kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar ya naɗa sabbin sarakunan ƙauyuka 17 daga sassan masarautar.

Waɗanda aka yiwa rawani sune Hakiman Kashi Koko, Mohammed Kudu; Somaji, Musa Ndace; Kolo Dzuru, Ibrahim Katamba da etson, Abubakar Alhassan.

Sauran sun haɗa da Zhiluko, Umaru Adamu; Kpatagi, Mohammed Kudu; Kagowogi, Zubairu Umaru; Emiwoshi, Ibrahim Zubairu; Daga, Aliyu Goyi; Mohammed Kudu, Ma’agi Buku; Alhaji Mohammed, Bazhi da Man Yahaya. Hakimin kauyen Gbade, Mohammed Baba; Patishi, Mohammed Gimba; Echegi, Yahaya Mohammed; Anfani Babban, Mohammed Sheshi; Saso Sunlati, Mohammed and Mana, Mohammed Saidu.

KU KUMA KARANTA: Daga hawansa gwamna Adeleke ya tsige sarakuna 3, ya kori ma’aikata 12,000

A yayin taron, Etsu Nupe ya baiwa sabbin sarakunan gargajiya aikin ba da fifiko kan tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummarsu.

A cewar Alhaji Abubakar, ta haka ne kawai yankunansu za su samu ci gaban da ake bukata.

Etsu Nupe ya buƙaci Hakiman ƙauyen da su jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya tare da yin adalci da gaskiya ga al’ummar yankunansu.

Ya ce sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen inganta zaman lafiya da tabbatar da adalci a matsayin hanyar taimaka wa gwamnatoci a dukkan matakai.

Etsu Nupe ya ce hakan na da matuƙar muhimmanci, duba da halin da ake ciki a halin yanzu na ɗimbin ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta da kuma irin manyan tsare-tsare na sarakunan gargajiya.

Don haka ya shawarci dukkan Hakiman Ƙauye da su zama jakadun zaman lafiya domin ci gaban masarautar Nupe baki ɗaya. Basaraken ya yabawa al’ummarsa bisa yadda suke zaune lafiya da juna, ya kuma buƙace su da su ci gaba da zaman lafiya a tsakanin jama’a.

A cewarsa, zaman lafiya yana da ƙima kuma yana da matuƙar muhimmanci a kiyaye shi domin ‘yan ƙabilar Nupe, jihar Neja da ma Nijeriya za su ci gaba.

Ya kuma yabawa al’ummar masarautar bisa goyon bayan da suke ba shi wajen samar da zaman lafiya, ya ƙara da cewa zaman lafiya shi ne tushen ci gaba.

Basaraken ya ce zaman lafiya da ake samu a yankin ya samo asali ne sakamakon ƙudurin da mutane suka yi na ganin sun haɗa kai don haka ya buƙace su da su ci gaba da fahimtar juna.

Ya buƙaci Nupawa da su yi watsi da ayyukan da za su iya ɓata sunan yankin.

Hakimin ƙauyen Somaji, Musa Ndace ya yi alƙawarin cewa ba za su gaza wajen sauƙe nauyin da ya rataya a wuyan Masarautar Etsu Nupe, Masarautar Bida da Jihar Neja ba.

Ya yabawa Etsu Nupe bisa wannan karramawar da ya yi musu. Ya kuma yi alƙawarin cewa za su yi duk mai yiwuwa na ɗan Adam wajen bunƙasa ci gaban yankunansu, Kin Nupe, Jihar Neja da Najeriya baki ɗaya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *