No menu items!

Sample Page Title

Date:

EFCC ta kama Tambuwal bisa zargin almundahanar Naira biliyon 189

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Jihar Sokoto kuma tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Aminu Waziri Tambuwal, kan zargin almundahanar naira biliyan 189.

Bisa ga rahotanni, an kama Tambuwal ne a yau yayin da ake gudanar da bincike kan yadda aka yi amfani da kudaden gwamnatin jihar a lokacin mulkinsa.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama ɗaliban Jami’ar Bayero 24, kan zargin aikata damfara ta Intanet

Majiyoyi daga hukumar EFCC sun tabbatar da cewa an tsare shi domin gudanar da cikakken bincike, yayin da ake ci gaba da samun ƙarin bayani game da lamarin.

EFCC ba ta bayar da cikakken bayani kan matakin da za ta ɗauka ba, sai dai rahotanni sun ce ana ci gaba da bincike kafin yanke hukunci.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...