EFCC ta kama mutane 23 da ake zargi da damfara ta yanar gizo

3
299

Jami’an Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati (EFCC) a Jihar Sakkwato, sun kai samame tare da cafke wasu mutane 23 da ake zargi da damfara ta Intanet da aka fi sani da ‘Yahoo boys’ a unguwar Bafarawa da ke cikin birnin Sakkwato.

Wata majiya daga ofishin shiyya na hukumar EFCC da ke Sakkwato ta ce baya ga yankin Bafarawa, an kuma kai samame a yankin kalkalawa jihar Sakkwato bayan binciken da jami’an leƙen asiri suka yi tare da sanya ido sosai ya tabbatar da cewa matasan na rayuwa fiye da yadda suke da ita ba tare da wata hanyar samun kuɗin shiga na gaske ba.

Hakan a cewar majiyar, ya sa jami’an hukumar suka kutsa kai tare da cafke su yayin da ake ci gaba da bincike.

KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC a Inugu, ta kama mutane 28 da ake zargi da damfara ta yanar gizo

Waɗanda aka kama sun haɗa da; Joy Ofem, Azeez O. Naimot, Ibrahim Amadu, Aigbekan Daniel, Adedayo Michael, Imran Mubaraq da Oliyide Habeeblah. Sauran sun haɗa da Wasiu Lukman Adekunle, Musa Abdulaziz, Abdullahi Ibrahim, Adejoh Nebiu Muhammad, Ibrahim Mubarak, Ahmed Ibrahim Abdullahi, Abdullahi senusi Adejoh da Umar Idris.

Cikin jerin sunayen akwai Muhammad Nuhu da Faisal Ahmed da Aliyu Ismail da Elijah Adebayo da Abubakar Bashir da Sakariya Ibrahim da Balogun Abdulayyan da kuma Buni Husaini.

Wasu daga cikin abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da; Red Corolla sport 2009 model, White Corolla 2015 model, 16 daban-daban laptops, 1 Generator, 30 daban-daban wayoyi da 2 MTN Routers.

Sai dai majiyar ta bayyana cewa za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.

3 COMMENTS

Leave a Reply