EFCC ta gayyaci shugaban NAHCON, Farfesa Saleh Pakistan kan zargin ɓatan Naira biliyan 50

0
0

EFCC ta gayyaci shugaban NAHCON, Farfesa Saleh Pakistan kan zargin ɓatan Naira biliyan 50

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta kaddamar da bincike a kan Farfesa Saleh Abdullahi Usman, Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), kan wasu makudan kudade da suka shafi ayyukan Hajji na 2025.

A cewar majiyoyi, Usman ya gabatar da kansa a hedikwatar EFCC da safiyar ranar Laraba, don amsa gayyatar da aka yi masa.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya umurci NAHCON ta rage kuɗin Hajjin bana

Daga baya an sake shi bisa beli amma ana buƙatar ya kai kansa Hukumar a kullum yayin da ake ci gaba da bincike.

Binciken ya biyo bayan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake ta tafkawa a cikin Hukumar, da suka haɗa da karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe da suka kai sama da Naira biliyan 50.

Leave a Reply