ECOWAS ta gindaya sharuɗa na cire wa Nijar takunkumai

0
190

Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta naɗa kwamiti na shugabanni uku da zai tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar kan mayar da mulki hannun farar-hula sannan ya duba yiwuwar janye takunkuman da aka kakaɓa wa ƙasar.

Shugabannin ƙungiyar ta ECOWAS sun bayyana haka ne a sanarwar da suka fitar bayan taronsu na shekara-shekara a Abuja ranar Lahadi.

ECOWAS ta naɗa kwamitin shugabannin ƙasashen Togo, Saliyo da Benin domin tattaunawa da sojojin Nijar don su amince “da jadawalin miƙa mulki a ɗan ƙanƙanin lokaci” sannan su “gaggauta dawo da tsarin mulki”.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun roƙi kotun ECOWAS ta tilasta wa makwabtan Nijar ɗage takunkumai

Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, da shugaban Benin Patrice Talon da kuma shugaban ƙasar Togo Faure Gnassingbe za su gana da sojojin na Nijar domin ganin “sun bar mulki a ƙanƙanin lokaci”, a cewar ƙungiyar.

ECOWAS ta ce: “Za a rika janye tankunkuman da aka sanya wa Nijar ne daki-daki bisa la’akari da sakamakon tattaunawar da kwamitin shugabannin ƙasashen ya yi da sojojin na Nijar”.

ECOWAS ta ce idan sojojin Nijar suka gaza bin ƙa’idojin da shugabannin ƙasashen uku da ke kwamitin suka ba su, ba za a cire wa ƙasar takunkumai ba kuma za a duba yiwuwar amfani da karfin soji.

Kazalika ƙungiyar ta jaddada ƙiran da ta yi wa sojojin Nijar na sakin Mohamed Bazoum da dukkan mutanen da suka kama ba tare da wani sharaɗi ba.

Tun da farko, shugaban Nijeriya Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban ECOWAS, ya ce ƙungiyarsu za ta yi ƙoƙarin tattaunawa da ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin soji domin mayar da mulki hannun farar-hula “a lokaci ƙanƙani”.

Leave a Reply