Connect with us

Ƙasashen Waje

ECOWAS ta damu kan ɗaga zaɓen shugaban ƙasa a Senegal

Published

on

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta nuna matuƙar damuwarta game da matakin da shugaban Senegal ta ɗauka na ɗaga babban zaɓen ƙasar.

Ranar Asabar Shugaba Macky Sall ya sanar da ɗage zaɓen ƙasar wanda aka tsara gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2024.

Ya sanar da hakan a wani jawabi da ya yi wa ƙasar a Dakar babban birnin ƙasar inda ya ce an ɗage zaɓen sakamakon wasu matsaloli da ke tattare da jerin sunayen ƴan takara.

A Nuwambar bara ne Mista Sall ya saka ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zaɓen ƙasar inda ƴan takara 20 za su fafata a zaɓen sai dai a cikin mutanen babu sunayen wasu manyan ƴan adawa.

Sai dai a jawabin da Sall ya yi a ranar Lahadi, ya ce ya saka hannu kan wata doka wadda ta yi watsi da hanyar da aka bi wurin saka ranar a baya inda ya ce ƴan majalisa za su gudanar da bincike kan wasu alƙalai biyu dangane da martabarsu sakamakon suna da alamar tambaya a tattare da su ta fuskar zaɓe.

KU KUMA KARANTA: Yau ce ranar zaɓen cike gurbi da raba gardama a jihohi 26 na Najeriya

Sall ya sha nanata cewa zai miƙa mulki a watan Afrilu zuwa ga wanda ya ci zaɓe.

Bayan sanar da cewa ba zai yi takara ba a karo na uku, Sall ya bayyana Firaiminista Amadou Ba wanda ɗan jam’iyyarsa ne a matsayin magajinsa.

Kotun ƙasar ta cire sunayen gomman ƴan takara da zaɓen daga ciki har da ɗan adawar nan Ousmane Sonko da Karim Wade, ɗan gidan tsohon shugaban ƙasar Abdoulaye Wade.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Asabar da maraice, ta bayyana “damuwa game da yanayin da ya sa aka ɗage zaɓukan” sannan ta yi ƙira ga “hukumomin da suka kamata su yi gaggawar kammala tsare-tsare domin a sanya sabuwar ranar zaɓe.”

Kazalika ECOWAS ta yi ƙira ga dukkan ‘yan siyasar Senegal su mayar da hankali wurin yin sulhu a tsakaninsu tare da haɗa kai wajen ganin an gudanar da sahihin zaɓe.

Haka kuma ƙungiyar ta jinjina wa Shugaba Salla bisa cika alƙawarin da ya ɗauka na ƙin sake tsayawa takara a zaɓen da ke tafe.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Published

on

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Frane Selak ya kasance wanda ya fi kowa tsallake rijiya da baya a duniya.

A shekarar 1962 ya tsallake haɗarin jirgin ƙasa wanda mutane 17 suka mutu, a 1963 jirgi ya faɗi da shi kowa ya mutu sai shi kaɗai ko ƙwarzane bai yi ba.

A shekarar 1966 motar safa ta lume da su a rafi mutum huɗu sun mutu amma Frane bai samu ko ƙwarzane ba a yayin da a shekarar 1973 motarsa ta kama da wuta ya tsallake rijiya da baya, ya kuma tsallake haɗarin taho mu gama da mota ta yi da shi ya tsira ya kuma lashe yuro dubu ɗari takwas a Caca a shekarar 2003.

KU KUMA KARANTA: Labarin zuwa Hajji mai ban mamaki

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Published

on

Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza, inda ta tilasta wa ɗaruruwan Falasɗinawa tserewa bayan da soji suka kuma ba da umarnin ƙaurace wasu yankuna masu yawan jama’a.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Isra’ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar

Waɗanda suka shaida lamarin sun ce an kai hari da dama a ciki da wajen birnin Khan Younis, inda aka hallaka mutane takwas kuma mutane sama da 30 suka samu raunuka, cewar wata majiyar lafiya da kuma ƙungiyar Red Crescent ta Falasɗinawa.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Published

on

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana - COPEC

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Man Fetur a Ghana ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar a samun ƙarin farashin man fetur a ƙasar a farkon watan Yulin 2024.

Ƙungiyar ta Chamber for Petroleum Consumers (COPEC) ta ce akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa farashin fetur da man dizel da gas zai ƙaru baki ɗaya a gidajen man da ke faɗin ƙasar, kamar yadda kamfanin watsa labarai na ƙasar Ghana ya ruwaito.

COPEC ɗin ta ce za a samu ƙarin farashin ne sakamakon yadda farashin Cedi ɗin a ƙasar ke ƙara karewa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

COPEC ɗin ta yi hasashen cewa farashin man fetur ɗin wanda za a rinƙa sayarwa a gidan mai zai ƙaru da kashi 2.17 cikin 100, wanda hakan ke nufin zai ƙaru daga Cedi 14.17 zuwa Cedi 15.20 a duk lita.

Sai kuma farashin dizel ana sa ran ya ƙaru zuwa 15.21 a kowace lita ɗaya, sai kuma na gas ya koma tsakanin Cedi 13.24 zuwa Cedi 14.64 a duk kilo ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya

Ƙungiyar ta COPEC ta bayar da shawara ga gwamnatin Ghana da ta yi duk mai yiwuwa domin rage harajin da yake a kan gas ko kuma yin tallafi a farashinsa domin bayar da dama ga ‘yan ƙasar su same shi a farashi mai rahusa.

Ta kuma yi ƙira ga gwamnati da kada ta yi ƙasa a gwiwa wajen dawo da matatar mai ta Tema a kan aiki (TOR) don kaucewa ko kuma rage shigo tattacen man fetur wanda a wani lokacin ake samun gurɓatacce.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like