ECOWAS ta buƙaci hukumomin Senegal su sanya ranar gudanar da zaɓe

0
108

Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi ƙira ga ƴan siyasar Senegalal su gaggauta ɗaukar matakai na sake fitar da ranar da za a gudanar da zaɓen ƙasar kamar yadda kundin tsarin mulkinsu ya tanada.

A farkon makon nan ne shugaban ƙasar Macky Sall kwatsam ya ɗage gudanar da zaɓen wanda aka tsara yi ranar 25 ga watan nan na Fabrairu zuwa watan Disamba.

Mista Sall ya ce ya ɗage zaɓen domin ganin an yi adalci bayan da aka cire sunayen wasu ƴan takara daga jerin masu tsayawa takara a zaɓen.

Wannan lamari dai ya haifar da tarzoma daga wurin ƴan ƙasar tare shan suka daga wurin jam’iyyun hamayya da ma ƙasashen duniya.

An kama tsohuwar Firaiministar Senegal Aminata Toure, wadda a yanzu ita ce babbar ƴar gaba-gaba a zanga-zangar nuna adawa da ɗage zaɓen shugaban ƙasa, ko da yake daga bisani an sake ta.

KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ta ɓarke a Senegal bayan sanar da ɗage zaɓe

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce tana bibiyar halin da ake ciki a Senegal cike da damuwa, sannan ta yi kira ga ƴan siyasa da ɗaukacin ƴan kasar su taimaka wajen ganin an wanzar da zaman lafiya.

“ECOWAS ta damu game da halin da ake ciki a Senegal. Tana bayar da shawarar kada a yi wani abu da zai saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar kuma tana tunatar da ƴan ƙasar da ƴan siyasa kan nauyin da ya rataya a wuyansu na wanzar da zaman lafiya,” in ji sanarwar.

Ranar Litinin, majalisar dokokin ƙasar ta gyara dokar zaɓen inda ta amince a gudanar da shi ranar 15 ga watan Disamba, sannan ta tsawaita wa’adin mulkin Mr Sall.

Tun da farko, an katse hanyoyin intanet a Dakar babban birnin Senegal da kuma sauran sassan ƙasar a daidai lokacin da ƴan majalisar ke shirin tafka muhawara kan ƙudirin da zai iya ƙara wa’adin mulkin Shugaba Macky Sall.

Leave a Reply