No menu items!

Sample Page Title

Date:

Durƙushewar Layin Lantarki: NMDPRA ta fara rabon lasisin iskar Gas

Hukumar kula da cinikayyar albarkatun man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta fara rabon lasisin cinikin iskar gas ga dillalan da suka cancanta a ɓangaren, sakamakon yawaitar durƙushewar babban layin lantarki na ƙasar.

An samu durƙushewar layin lantarkin sau ɗaya ne tak a sabuwar shekarar da muke ciki bayan da ya durƙushe fiye da sau 10 a 2024, abin da ya jefa sassan Najeriya da dama cikin duhu na sa’o’i masu yawa.

KU KUMA KARANTA:Hari kan layin wutar lantarki ya jefa Abuja cikin duhu

Sanarwar da sashen yada labarai na NMDPRA ya fitar a yau Litinin dauke da sa hannun Jamilah Adama, yace al’amarin ya dace da umarnin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da cewa dukkanin tashoshin samarda lantarki na samun iskar gas din da suke bukata domin karfafa aikin fadada tsarin rarraba lantarkin da ake da shi a halin yanzu.

Sai dai hukumar ta gargadi dukkanin dillalan su tabbatar da dorewar samar da iskar gas kamfanonin samar da lantarkin ko kuma a soke lasisin nasu kasancewar ba za’a lamunci ayyukan zagon kasa ba,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...