Duniya ce ta gina Majalisar Ɗinkin Duniya, domin hidimta wa al’ummar duniya – António Guterres

0
54
Duniya ce ta gina Majalisar Ɗinkin Duniya, domin hidimta wa al’ummar duniya - António Guterres

Duniya ce ta gina Majalisar Ɗinkin Duniya, domin hidimta wa al’ummar duniya – António Guterres

A cikin sakon sakatare janar na MƊD a ranar bikin Majalisar Ɗinkin Duniya ta 2024.

Tun daga 1945, ya zama an tsara wasu ƙasashe da za su samar da mafita da haɗin kai domin magance matsalolin duniya da samar da zaman lafiya.

Mafitar da za ta kawo sassaucin tashe-tashen hankula, da kuma gina hanyoyin da za su wanzar da zaman lafiya.

Ba wani abu ne mafita illa kawar da fatara, da zaburar da ci gaba mai dorewa, da tsayawa domin ganin an taimaki masu rauni.

Mafitar da ke ba da agajin ceton rai ga mutanen da ke rayuwa a yankunan da ke fama rikice-rikice, tashe-tashen hankala, matsalolin tattalin arziki da bala’o’in sauyin yanayi.

Mafitar da ke daidaita ma’aunin adalci da daidaito ga mata da ‘yan mata.

KU KUMA KARANTA: MƊD ta ƙaddamar da bugu biyu na Muryoyin Sahel;

Hanyoyin da ke magance batutuwan da ba za su iya misaltuwa ba tun da 1945, canjin yanayi, fasahar dijital, basirar wucin gadi, da sararin samaniya.

A cikin Satumba, Babban Taro ya amince da Yarjejeniya domin ci gaban Ka’idar Dijital ta Duniya da Sanarwa kan Karni mai zuwa.

Wadannan muhimman yarjejeniyoyin za su taimaka wajen tabbatar da cewa tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya ya daidaita gyare-gyare da sake sabuntawa, don haka ya dace da sauye-sauye da kalubalen da ke kewaye da mu da kuma samar da mafita ga kowa.

Amma aikinmu zai kasance a koyaushe mai tushe a cikin dabi’u da bin ka’idodin Yarjejeniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya da dokokin ƙasa da ƙasa, da kuma mutunta ‘yancin ɗan’Adam na kowane mutum.

A cikin duniya mai wahala a yau, har yanzu ba a cimma wannan burina ba

Fatanmu bukatar yunkurin aiki da hanyoyin magance rashin zaman lafiya, wadata juna da bunkasa duniya.

Burinmu shi ne, tabbatar da bukatar duk kasashe su yi aiki kafada-da kafada.

Wannan shi ne abin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke bukata.

A wannan rana ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ina kira ga dukkannin ƙasashe da su kiyaye wannan haske ga duniya, da manufofinta ke haskakawa.

Leave a Reply