Duk Abin Da Yake Mai Kyau Da Zai Amfani ‘Yan Najeriya Shugaba Buhari Zai Sa Hannu – Sanata Gobir

0
314

…Don Haka Muna So A Kirkiri Hanyoyin Sarrafa Makamashin Da Mu Ke Dasu Domin Amfanin Al’umma.


Daga; USMAN NASIDI.

SANATA Ibrahim Abdullahi Gobir, mai wakiltar Jihar Sokoto ta gabas a Majalisar Dattawa, ya bayyana cewa babu wani abu mai kyau da amfani wanda za a kai shugaban kasa Muhammadu Buhari da ba zai aminta da sa hannu a kai ba muddun idan zai amfani al’ummar Kasar Najeriya.

Sanata Ibrahim Gobir, wanda shi ne shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa sannan kuma mataimakin shugaban kwamitin kasuwanci da saka hannun jari a Majalisar Dattawan, ya furta hakan ne a wani zantawarsa da manema labarai a garin Abuja.

Ya kara da cewa wannan kudirin da ya kawo kana ya gabatar domin Sarrafa makamashin da ake da su a kasar, wani abu ne wanda zai amfani yan Kasar baki daya, sannan da tabbatar da an samu ci gaba ta fannin raya kasar Najeriya da al’ummar ta da abubuwan more rayuwa.

Ya ce “kowani irin makamashi muke amfani da shi yana cikin wannan kudirin domin babu wani abu wanda baya ciki. kun ga idan muna maganar Gawayi, Man Iskar Gas, Man Fetur, Wutan Lantarki, Wutar Hasken Rana, Danyen Mai da duk wasu abubuwan da ake tsammani duk suna cikin wanda hakan zai inganta al’amuran mu ko da ta fannin Wutan Lantarki ne ba za a samu matsala ba.”

“Amma yanzu ace kamar Najeriya, wuta ma babu, komai babu kuma kowani irin makamashi ake magana babu shi, toh kun ga ko akwai matsala, duk da cewa dama akwai wata cibiya ta wuta wacce ita ce ya kamata ta rika zakulo duk irin wadannan abubuwan daya bayan bayan ana Sarrafa su.”

A cewarsa, kirkirar wasu abubuwan da za a rika amfani da su domin sarrafawa sinadarin Carbon Monoxide wani abu ne wanda zai taimaka wa fannin samar da abubuwan da ake bukata a cikin kasar wadanda al’umma za su samu ci gaba ta fannin samun saukin gudanar da rayuwa.

A karshe, Sanata Ibrahim Gobir, ya bayyana cewa Allah Ya albarkace mu da duk wasu abubuwan da muke bukata domin samun Ingantaccen rayuwa, kana yana saran shugaba Buhari zai saka hannu a takardar kudirin muddun idan ya fahimci lamarin na da matukar alfanu ga al’umma da Kasar baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here