Dubban sojojin Isra’ila sun kamu da cututtuka a Gaza.

0
169

Hare-haren da Isra’ila ta kwashe kwana 86 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasɗinawa akalla 21,672 tare da jikkata 56,165 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn ‘yan gudun hijira.

Ana zargin gomman sojojin Isra’ila waɗanda aka jibge kusa da Zirin Gaza da kamuwa da wata cutar fata mai suna leishmaniasis, kamar yadda wata jaridar Isra’ila ta bayyana a ranar Lahadi.

Jaridar ta bayyana cewa akwai sojoji da dama da aka aika da su domin yi musu gwaji, duk da cewa har zuwa yanzu sakamakon gwajin bai fito ba, inda wasu tuni aka aika da su sashen kula da fata domin yi musu magani.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin na Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a cikin Zirin Gaza inda suke kashe yara da mata.

Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin sake ƙwace ikon gudanar da iyakar Gaza da Masar, a yayin da adadin Falasɗinawan da dakarunsa suka kashe ya zarta 21,670.

“Yaƙin nan ya kai kololuwa,” in ji Netanyahu a hira da manema labarai, inda yake magana a kan ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta kai harin ba-zata Isra’ila inda ta kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da mutum 240.

KU KUMA KARANTA: Yawan Falasɗinawan da aka kashe a hare-haren Isra’ila sun kai 21,500 — Ma’aikatar Lafiya ta Gaza

Ya ƙara da cewa dole ne yankin Philadelphi da ya ratsa iyakar Gaza da Masar ya kasance a hannun Isra’ila.

“Dole a toshe yankin,” a cewar Netanyahu. “A bayyane yake cewa babu wani shir da zai kawar da hare-haren da muke so a daina kaiwa.”

Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant da Ministan da ke Jagorantar Yaki Benny Gantz sun ki halartar taron manema labarai da Firaiminista Benjamin Netanyahu ya gudanar ranar Asabar da maraice.

Hukumar watsa labarai ta Isra’ila ta wallafa sako a shafin ta na X da ke cewa Gallant da Gantz sun ki halartar taron ne ba tare da bayyana dalilin hakan ba.

Babu wata sanarwa da mutanen uku suka fitar a game da wannan batu, ya zuwa karfe shida da minti arba’in a agogon GMT.

Benjamin Netanyahu yana shan suka daga wani bangare na majalisar ministocinsa kan yaki a Gaza.

Mun kashe ƙarin sojojin Isra’ila 20 tare da jikkata wasu a Gaza acewar dakarun Al Qassam Brigades

Al Qassam Brigades, wanda shi ne ɓangaren sojoji na ƙungiyar Hamas, yace dakarunsa sun kashe sojojin Isra’ila sama da 20 tare da jikkata da dama a wani gumurzu da suka yi a Birnin Gaza.

A wani sako da ya wallafa a manhajar Telegram, Al Qassam Brigades ya ce mayakansa sun yi arangama da dakaru na musamman na Isra’ila da ke “kutsawa yankin Sheikh Radwan da ke Birnin Gaza, lamarin da ya kai ga kisan sojoji fiye da 20 tare da jikkata wasu.”

A wani sako na daban, ɓangaren sojin na Hamas ya ce mayakansa sun kai hari kan “tankar yakin Isra’ila ta Merkava da abubuwan fashewa na Sho’ath a yankin Sheikh Radwan na Gaza.”

Kazalika mayaƙan Al Qassam Brigades sun yi amfani da makamai masu linzami suka ragargaji “wani jerin gwanon ababen hawa na Isra’ila da kuma sojojin ƙasar a birnin Khan Yunis na kudancin Zirin Gaza.”​​​​​​​

Leave a Reply