Dubban Falasɗinawa sun tsere daga wani yanki a tsakiyar Gaza

0
39
Dubban Falasɗinawa sun tsere daga wani yanki a tsakiyar Gaza

Dubban Falasɗinawa sun tsere daga wani yanki a tsakiyar Gaza

Dubban Falasɗinawa sun tsere daga wani yanki a tsakiyar Gaza sakamakon sabbin umarnin ficewa da Isra’ila ta yi, lamarin da ke ƙara ta’azzara halin jinƙai a wani yanki da tuni ya cika da ‘yan gudun hijirar da ke tsere wa farmaki a kudancin ƙasar.

Sojojin Isra’ila, waɗanda a yanzu suka ƙwace kusan ɗaukacin yankunan a cikin kusan watanni 10 na yaƙin, sun shafe makonni da dama suna ƙaddamar da manyan hare-hare a yankunan da a baya suka yi ikirarin “kore mayaƙan Hamas.”

A harin na baya-bayan nan da ta kai, Isra’ila ta umarci mazauna garin a ranar Lahadi da su ƙaurace wa Al-Bureij da ke arewa maso gabashin Deir.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila tana shirin kai farmaki a wani sansanin ‘yan gudun hijira a Gaza

“Me ya saura? Deir? Deir cike take da mutane, kowa yana Deir, duk Gaza. Ina mutane za su tafi?” Aya Mansour ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a Deir bayan ta gudu daga Bureij.