DSS ta rufe ofishin PDP na Ondo kan ɓacewar gwamnan jihar

0
188

Jami’an DSS da ’yan sanda sun rufe ofishin PDP na Ondo, inda jama’a ke neman gwamnatin jihar ta bayyana inda Gwamna Akeredolu ya shige.

Jami’an tsaron DSS da kuma ’yan sanda sun rufe sakatariyar jam’iyyar adawa ta PDP ta Jihar Ondo.

Hukumomin tsaron sun ɗauki matakin ne a safiyar Litinin a daidai lokacin da al’ummar jihar suke gunaguni da neman gwamnatin jihar ta bayyana musu inda Gwamna Rotimi Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki.

Ana zargin hukumomin tsaron sun rufe ofisihin jam’iyyar ne sakamakon shirin wasu ’yan jam’iyyar na gudanar da zanga-zanga kan rashin kasancewar gwamnan a jihar na tsawon lokaci.

KU KUMA KARANTA: DSS ta kama babban Editan jaridar Almizan a filin jirgin sama na Kano

Da farko Gwamna Akerodule wande ke fama da rashin lafiya da ba a bayyana ba, ya shafe wata uku a ƙasar Jamus, inda yake jinya, kafin ya dawo jihar a watan Satumba.

Tun bayan dawowar gwamnan, ya ci gaba da zama a gidansa, da ke birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, lamarin da ya sa babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar ƙiraye-ƙirayen ya sauƙa daga muƙaminsa.

A ranar Lahadi PDP ta yi barazanar jagorantar wani gagarumin zanga-zanga a birnin Akure a yau Litinin, domin neman sanin inda Mista Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki da ya hana shi zama a Jihar Ondo.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin samun ƙarin bayani kan halin da ake ciki daga kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo Funmilayo Odunlami-Omisanya, amma haƙar ba ta cim-ma ruwa ba.

Leave a Reply