Hukumar tsaro ta farin kaya, (DSS) ta kama tare da tsare mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya mai kula da harkokin kuɗi, Aisha Ahmad, bisa zarge zargen damfarar hannun jari a bankin Polaris, Titan Bank da Union Bank.
Wata majiya a rundunar ‘yan sandan sirri ta shaida wa ‘News Point Nigeria’ cewa, a halin yanzu ana yi wa Mataimakiyar Gwamnan CBN tambayoyi kan yadda Bankin Titan Bank ya tara dala miliyan 300 don kammala sayan Bankin Union.
A cewar majiyar, sashen ya kuma ƙwace kayan lantarki na Ahmad tare da kwashe wasu takardu daga gidanta da ofishinta.
Har yanzu Ahmad tana nan a Sashen har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.