DSS ta dakatar da zaɓen NURTW

Jami’an hukumar tsaro na farin kaya sun kai farmaki garin Lafiya a jihar Nasarawa a daren ranar Laraba domin hana ƙungiyar Direbobi ta NURTW gudanar da taron wakilanta, inda suka bayyana shi a matsayin haramtacce.

A makon da ya gabata ne rundunar ‘yan sanda a Abuja ta cafke shugaban ƙungiyar Alhaji Tajudeen Ibikunle Baruwa bisa zargin shigo da ‘yan daba da ‘yan bindiga a cikin babban birnin tarayya.

Hakazalika jami’an tsaro sun rufe Sakatariyar ƙungiyar ta ƙasa domin hana taɓarɓarewar doka da oda.

An hana su amfani da Sakatariyar wajen zaɓen. A ƙoƙarin kawar da shi daga hannun jami’an tsaro ne ‘yan ƙungiyar a ranar Larabar da ta gabata sun hallara a garin Lafiya na jihar Nasarawa domin gudanar da zaɓen, amma jami’an tsaro sun hargitsa lamarin inda kowa da kowa ciki har da shugabannin ƙungiyar suka gudu don gudun ka da a kama su.

Wani ɓangare na ƙungiyar ya ba da umarnin kotu wanda ya umurci ƙungiyar da ta ci gaba da kasancewa a halin yanzu har sai an saurari ƙarar da kuma tantance.

KU KUMA KARANTA: DSS sun cafke matashin malamin nan Malam Baffa Hotoro a jihar Kano

Idan dai za a iya tunawa, shugabannin ƙungiyar a yankin Kudu maso Yamma sun kasance kan gaba wajen tayar da jijiyar wuya na neman wa’adi na biyu na shugaban su mai ci Alhaji Baruwa, don haka ne aka gurfanar da shi a gaban kotu domin tantance cancantar sa na tsayawa takara.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *