DSS sun cafke shugaban ƙungiyar Miyatti Allah

0
132

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani a jihar Nasarawa.

Wasu shugabannin ƙungiyarsa ta Kautal Hore kuma makusanta sun tabbatar da batun kama Bodejo a jiya Talata.

Sun ce jami’an DSS tare da wasu sojojin Najeriya suka kama shi a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa.

Sai dai sun ce suna bin bahasi domin ba su san inda aka tafi da shi ba.

A ranar Laraba 17 ga watan Janairu Bello Badejo ya ƙaddamar da rundunar a garin Lafiya inda ya ce za ta taimaka wajen yaƙar ɓarayi da ɓata-gari daga cikin Fulani.

KU KUMA KARANTA: An ɗaure Sarkin Fulani da ‘yan uwansa 2 kan garkuwa da mutane

Bayanai na cewa jami’an tsaron Najeriya sun kama Bodejo ne kan fargabar cewa ƙirƙiro da ƙungiyar sa-kai zai iya janyo tashin hankali a faɗin ƙasar, kuma kasancewar ba ta da rijista da hukumar farin kaya ta DSS.

Leave a Reply