DSS sun cafke matashin malamin nan Malam Baffa Hotoro a jihar Kano

Jami’an tsaron farin kaya na DSS a Kano sun cafke matashin malamin nan Baffa Hotoro da ake zargi da yin sakin baki ga Manzon tsira (s.a.w)

A watan azumin da ya gabata ne Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da cewa an kama matashin amma daga bisani Baffan ya fito a bidiyo ya musanta cewa an kama shi.

Amma a Alhamis ɗin nan hukumar DSS a Kano ta tabbatar wa da Jaridar Idaniya cewa suna tsare da Baffa Hotoron.


Comments

2 responses to “DSS sun cafke matashin malamin nan Malam Baffa Hotoro a jihar Kano”

  1. […] KU KUMA KARANTA: DSS sun cafke matashin malamin nan Malam Baffa Hotoro a jihar Kano […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: DSS sun cafke matashin malamin nan Malam Baffa Hotoro a jihar Kano […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *