Dole sojojin Najeriya su koyi harsunan gida don samun sahihan bayanan sirri — COAS
Daga Jameel Lawan Yakasai
Babban Hafsan Sojojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya shawarci jami’an Sojojin Najeriya da su ci gaba da koyon yarukan gida da suka samu yayin horo, yana mai cewa wannan muhimmin makami ne wajen tattara bayanan sirri.
Janar Oluyede ya yi wannan kira ne a yau Juma’a a birnin Abuja, yayin bikin kammala horo kan koyon harsunan gida karo na 7/2025 da aka gudanar a cibiyar horar da Sojojin Najeriya (Nigerian Army Resource Centre – NARC).
Babban Hafsan Gudanarwa na Sojojin Ƙasa, Manjo Janar Lawrence Fejokwu me ya wakilci COAS din a wajen taron.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe mataimakin Turji da wasu mayaƙansa da dama
Ya ce: “Dukkan ayyukanmu sun ta’allaka ne da bayanan sirri, kuma ingancin bayanan sirri yana dogara da yadda ake iya sadarwa da al’ummar wuri.”
Ya ƙara da cewa samun kwarewa a harsunan gida zai ƙara yarda tsakanin sojoji da al’umma, ya inganta sadarwa, tare da ƙarfafa ƙoƙarin yaki da kuma dakile barazanar tsaro a ƙasar.









