Dole ne mu yi amfani da fasahar zamani wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihohinmu – Gwamnan Zamfara

0
463

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamna Dauda Lawal ya jaddada buƙatar amfani da manyan na’urorin zamani domin yaƙi da matsalar tsaro a jihar Zamfara da ma arewacin Najeriya.

Gwamnan jihar Zamfara da wasu gwamnonin jihohi sun gana da Amina J. Mohammed mataimakiyar babban sakataren majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Washington D.C. ranar Juma’a.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta bayyana cewa taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Zamfara, Benuwe, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, da Neja.

Mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J. Mohammed ta yabawa Gwamnonin kan ƙoƙarin da suke yi na ganin an magance matsalolin yankin. “Kasancewar ku a nan ya nuna ƙwaƙƙwaran sha’awar da Gwamnonin Arewa ke yi na aiwatar da sauyi a jihohinsu.

Da yake bayyana halin da ake ciki a Zamfara ga Mataimakin Sakatare Janar, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana muhimmiyar rawar da fasaha za ta iya takawa wajen inganta tsaro da kuma buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen amfani da ƙarfin fasahar da ta haɗa da yin amfani da fasahar ƙere-ƙere, na’urorin tantance ƙwayoyin halitta da kyamarorin sa ido.

KU KUMA KARANTA: Mun inganta hanyoyin tafiyar da gwamnatinmu – Gwamnan Zamfara

“Babban ƙalubale shi ne rashin tsaro, kuma dole ne a yi wani abu.

“Saboda rashin tsaro, noma ya gagara. Muna buƙatar taimako wajen sauya sheƙa daga noman manoma zuwa bunƙasa noma ta yadda za mu iya tura fasahar yaƙi da wannan ta da ƙayar baya. Muna fatan samun mafita ga waɗannan matsalolin yayin waɗannan tarukan.

“Na ayyana dokar ta ɓaci a fannin ilimi da lafiya. Dole ne mu ɗauki matakin gaggawa don magance waɗannan batutuwa masu mahimmanci, in ba haka ba, makomarmu za ta yi rauni. Muna buƙatar tallafi mai mahimmanci don shawo kan waɗannan ƙalubalen da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga jama’armu.”

Leave a Reply