Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya tuna da ranar ‘yan jarida da ke bakin aiki, inda ya bayyana cewa dole ne a rika faɗin gaskiya a kafafen yaɗa labarai, idan har ana son a samu duniya mai walwala da zaman lafiya.
A wata sanarwa da Sashen Sadarwar ya fitar a ranar Laraba, Altun ya jaddada cewa “ɗaya daga cikin manyan matsalolin duniya a yau shi ne ‘Rikicin Faɗin Gaskiya’ inda labaran ƙarya suka zama babban ƙalubale a faɗin duniya.
Ya ce duk da cewa ana samun ƙarin damarmakin sadarwa a kowacce rana da yadda ake samun bayanai cikin sauki, akwai babbar buƙatar samun sahihan bayanai tsantsa kuma a cikin sauki.
Altun ya ƙara da cewa “Ya kamata a girmama tare da jinjina wa duk ‘yan jaridar da ke aiki da ka’idojin faɗar gaskiya na aikin jarida, sannan a amince da su a matsayin masu sana’a mai daraja a idon duniya.”
“Muna duba tabbatar da faɗar gaskiya a kafafen yaɗa labaran da ke ƙasarmu da ma fagen ƙasa da ƙasa a matsayin ɗaya daga cikin jigogin samun zaman lafiya da walwala a duniya.”
Daraktan Sadarwar ya kuma yi addu’a ga ‘yan jaridar da suka rasa rayukansu a yayin da suka tsaka da aiki, musamman a Gaza.
KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe ‘yan jarida 106 a yakin da take yi a Gaza — Jami’ai
“Abin takaici, rikicin Gaza da aka fara tun 7 ga Oktoba na bayyana ‘yan jarida, da ke aiki mai hatsari ga ɗan’adam, ba sa samun hakkinsu na rayuwa, ballantana a yi maganar hakkin faɗin albarkacin baki, ko na karɓar bayanai,” in ji Altun yayin da yake sukar hare-haren Isra’ila.
Sama da ‘yan jarida 100 Isra’ila ta kashe, sannan ta jikkata wasu da dama a hare-haren da take kaiwa yankin Falasdinu da aka yi wa kawanya.
Ya sha alwashin cewa sashen sadarwar zai ci gaba da kare hakkoki da dokokin da suka shafi ‘yan jarida, kare rayukansu, da taimaka musu a yayin da suke tsaka da aiki.
Altun ya ce “Ina taya murnar ’10 ga Janairu Ranar ‘Yan Jarida da ke Aiki’ da dukkan ma’aikatan kafafen yaɗa labarai da ke aiki dare da rana suna sadaukarwa, suna yunƙurin yin aikinsu da gaskiya da amana, kuma ba sa yadda su kauce hanyar gaskiya.”