No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi ƙira ga takwarorinsa na Chaina, Turkiyya, da sauran ƙasashe su “hana Iran mayar da martani” bayan Isra’ila ta kai hari a ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Damascus

Blinken ya yi magana ta wayar tarho da takwarorinsa na China, Turkiyya, Saudiyya, da Tarayyar Turai inda ya “bayyana musu ƙarara cewa bai kamata a ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya ba sannan ya buƙace su da su yi kira ga Iran kada ta mayar da martani,” a kamar yadda kakakin Ma’aikatar Wajen Amurka Matthew Miller ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis.

Kazalika Blinken ya yi magana ta wayar tarho da Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant “domin jaddada goyon bayanmu mai ƙarfi ga Isra’ila kan duk wata barazana da za ta fuskanta,” in ji Miller.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe manyan jami’an sojin Iran a harin da ta kai ta sama

Iran ta sha alwashin mayar da martani bayan Isra’ila ta kai hari a ƙaramin ofishin jakadancinta a Damascus ranar 1 ga watan Afrilun, inda ta kashe zaratan sojoji bakwai na runduna ta musamman ta Revolutionary Guards, cikinsu har da janar-janar guda biyu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...