Dole a dakatar da kisan ƙare dangi ba tare da ɓata lokaci ba a Gaza – Fidan

0
60

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya jaddada wa Sakataren Waje na Amurka Antony Blinken buƙatar cewa dole ne a dakatar da kisan ƙare dangin da ake yi a Gaza ba tare da ɓata lokaci ba.

Ya jaddada masa hakan ne a wata ganawa da suka yi a birnin Riyadh na Saudiyya a ranar Litinin, inda Fidan ya ce dole a matsa wa Isra’ila lamba don kawo ƙarshen kisan ƙare dangin, ta hanyar tsagaita wuta ta dindindin, da kuma kai kayan agaji Gaza.

Fidan da Blinken sun tattauna a kan abin da ke faruwa a Gaza a baya-bayan nan, kamar yadda majiyoyin diflomasiyya suka ce.

Sun kuma tattauna kan halin da ake ciki a yanzu a Ukraine da kuma dangantakar diflomasiyyar da ke tsakanin Ankara da Washington.

KU KUMA KARANTA: Kwamitin Tuntuɓa kan Gaza, da Turkiyya sun tattauna kan zamowar Falasɗinu ƙasa mai ‘yanci

Fidan da Blinken sun yi ƙwarya-ƙwaryar ganawar ne ta masu ruwa da tsaki a lamarin Gaza, a wani ɓangare na Babban Taron Tattalin Arziki na Duniya, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Turkiyyan ya wallafa a shafin X.

An samar da ƙungiyar masu ruwa da tsaki kan Gaza ta Gaza Contact Group ne a wani taron Ƙungiyar Ƙasashen Musulmai OIC da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa a watan Nuwamba don dakatar da rikicin da ake yi a Gaza da kuma taimakawa wajen cimma zaman lafiya na dindindin.

Isra’ila ta ƙddamar da mummunan yaƙi a kan Falasɗinu tun bayan da ƙungiyar Hamas ta kai mata wani harin ba-zata ranar 7 ga watan Oktoban bara.

An kashe Falasɗinawa kusan 34,500 tun lokacin, waɗanda mafi yawansu mata ne da yara, sannan an jikkata fiye da mutum 77,600, tare da lalata gine-gine da abubuwan more rayuwa, lamarin da ya jawo fama da ƙarancin abubuwan buƙata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here