Dokar Haraji: Babu wani tanadi na talauta Arewacin Najeriya – Tinubu

0
39
Dokar Haraji: Babu wani tanadi na talauta Arewacin Najeriya - Tinubu

Dokar Haraji: Babu wani tanadi na talauta Arewacin Najeriya – Tinubu

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi magana a kan ƙudurin dokar haraji da ake ta ce-ce-ku-ce a kanta a cikin makonnin nan, inda a ranar Litinin ta ce ƙudurin bai ƙunshi batun soke hukumomi irin su TETFUND da NASENI da NITDA ba.

A sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan watsa labarai Bayo Onanuga, ta ce a maimakon haka, sauye-sauyen na da nufin daidaita tsarin harajin Najeriya, da rage nauyi a kan ‘yan kasuwa da kuma bunƙasa zuba jari.

Tun bayan da batun ƙudurin sabuwar dokar harajin ya bayyana, ‘yan ƙasar suke ta muhawara kan alfanunta da kuma akasin haka.

Amma sanarwar Fadar Shugaban Ƙasa ta jaddada cewa ƙudurorin sun rage biyan haraji gutsul-gutsul zuwa a dunƙule don tabbatar da cewa hukumomi sun ci gaba da samun kudade ta hanyar tanadin kasafin kuɗi.

Sauye-sauyen, in ji Onanuga, an tsara su ne don sabunta dokokin haraji da suka tsufa, tare da haɓaka ci gaban ƙasa ba tare da an talauta kowane yanki ba.

KU KUMA KARANTA: Za mu tabbatar Majalisa ta yi watsi da dokar haraji – Tambuwal

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Kudirin sake fasalin haraji ba zai sa Legas ko Ribas su fi sauran jihohin kasar wadata ba, kamar yadda ake yayatawa. Kudirin ba zai lalata tattalin arzikin kowane sashe na ƙasar ba.

“A maimakon haka, suna da burin inganta rayuwar ‘yan Najeriya, musamman ma marasa galihu, waɗanda ke ƙoƙarin samun abin rufin asiri.

Sabanin ƙaryar da ake yaɗawa, ƙudurorin ba su nuna cewa za a rushe hukumomi irin su NASENI,da TETFUND, da NITDA ba nan da shekarar 2029 bayan an zartar da ƙudirin.

Leave a Reply