Connect with us

Labarai

Dillalan magani sun shiga yajin aiki a Kano

Published

on

Ƙungiyar ’yan kasuwa masu sayar da magani (NAPPMED) sun shiga yajin aiki a jihar Kano har sai abin da hali ya yi.

’Yan maganin sun dakatar da harkokinsu ne bayan Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta rufe musu shagun a Malam Kato da kuma Kasuwar Sabon Gari.

Sun sanar da shigarsu yajin aikin ne bayan sun yi, sallah tare yin addu’o’in samun nasara daga Allah a shari’ar da ke tsakaninsu da hukumar.

NAFDAC ta rufe shagunan ’yan maganin ne da ke Malam Kato da kuma cikin Kasuwar Sabon Gari a Jihar Kano.

Shugaban NAFDAC a jihar, Kashim Ibrahim, ya ce sun rufe shagunan ne domin ganin ’yan maganin sun bi doka ta hanyar komawa Kasuwar Dangwaro.

A cewarsa, za a ci gaba da samar da shagunan a Kasuwar Dangwaro domin magance matsalar rashin isassun shagunan da ’yan maganin suke fakewa da ita a matsayin dalilin rashin komawarsu kasuwar.

Amma a martaninsa, shugaban ƙungiyar a jihar, Muhammad Musbahu Khalid, ya bayyana cewa sabon wurin da ake so su koma na Dangwaro ba na gwamnati ba ne, kawai na wasu ne domin tsawwalawa ’yan kasuwar magani.

KU KUMA KARANTA: Masu Biredi a Najeriya na shirin tsunduma yajin aiki saboda tsadar kayan hada Biredi

A cewarsa sun rufe shagunansu ne domin gwamnati ta san amfanin ’yan magani a jihar Kano.

“Mun ɗauki wannan mataki ne don nuna wa gwamnati fushinmu da rashin amincewarmu game da hukuncin da kotun ta yi. Hakan zai sa gwamnati ta san amfaminmu.

Ya ci gaba da cewa ƙungiyar tasu za ta ɗaukaka ƙara don kalubalantar hukuncin kotun.

“Daga lokacin da aka yanke hukuncin mun karɓi kwafin shari’ar inda kuma lauyoyinmu suka garzaya kotun daukaka kara don kalubalantar hukuncin; kuma insha Allah za mu yi nasara a kotun gaba.”

Ya kuma yi watsi da batun da ake yi cewa ’yan kabilar Ibo ne masu sana’ar magani a Kano, inda ya ce, “Wannan zance ne maras tushe kuma zalinci ne. Muna so al’ummar jihar manyanta da kakana su sani an yi haka ne saboda zalunci.”

Musbaha Yahaya, ya ba wa marasa lafiya hakuri da cewar, lamarin ya faru ne ba don suna so ba, sai don ya zame musu dole.

Idan za a iya tunawa a ranar Juma’ar da ta gabata ne Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ƙarƙashin jagorancin Mai sharia Simon Amobeda ta umarci manyan dilolin maganin da su koma Kasuwar Dangwaro don ci gaba da kasuwancinsu.

Hukuncin kotun shi ya kawo ƙarshen takaddamar da aka ɗauki tsawon shekaru biyar ana yi tsakanin hukumar NAFDAC da kuma ƙungiyar ’yan kasuwar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like