Connect with us

Al'ajabi

Dattijo ɗan shekara 80 ya mutu a cikin rijiya a Kano

Published

on

Wani dattijo mai shekaru 80 mai suna Malam Rabiu wanda aka fi sani da Na-Allah Siraka ya rasu a wata rijiya da ke Sabon Sara, Gidan Aminu Ado da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya raba wa manema labarai ranar Lahadi a Kano.

Malam Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi. “Mun samu ƙiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:00 na safe daga wani Hassan Abduallhi, cewa wani mutum ya maƙale a cikin rijiya.

KU KUMA KARANTA: Ya mutu a ƙoƙarin ɗauko wa wasu mata zanin su a rijiya

“Nan da nan muka aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin ƙarfe 11:07 na safe,” in ji shi. Malam Abdullahi ya ce Malam Rabiu ya zauna shi kaɗai a gidansa.

PRO ya ce jami’an kashe gobara sun fito da gawar Rabiu daga cikin rijiyar da ta mutu,” inji shi.

Kakakin ya ce an miƙa mamacin ga Hakimin unguwar Sabon Sara, Muhammad Salisu-Iman.

Malam Abdullahi ya ce ana kan binciken musabbabin faruwar lamarin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

An ƙona mutane suna Sallar Asuba a masallaci a Kano

Published

on

An ƙona mutane suna Sallar Asuba a masallaci a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta yayin da mutane ke Sallar Asuba ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Gadan da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a jihar ta Kano, da misalin karfe 5:20 lokacin da ake sallah, a cewar sanarwa ‘yan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa da TRT Afrika Hausa faruwar lamarin da kama mutumin da ake zargi, sai dai ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

Abdullahi Kiyawa ya ce bincike ya nuna cewa mutumin da ake zargi da cinna wutar Shafi’u Abubakar mai kimanin shekaru 38 ya jefa wata roba ne ɗauke da fetur cikin masallacin, sannan ya cinna wuta.

KU KUMA KARANTA: Mahara a Anambara sun ƙona fadar babban Basarake ƙurmus

Kakakin ‘yan sandan ya ce mutum 24 ne suka ƙone a masallacin, da suka haɗar da manya 20, yara huɗu.

An garzaya da duka waɗanda suka jikkata zuwa asibiti don ba su kulawa, amma babu wanda ya mutu a haɗarin, a cewar sanarwar ‘yan sandan.

Continue Reading

Al'ajabi

An tsinci gawar wata ɗaliba a cikin ɗaki a Kano

Published

on

An tsinci gawar wata ɗaliba mai suna Aisha Yahaya ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil, a wani gida da ke wajen jami’ar.

Aisha, ɗaliba ce da ke matakin karatu na uku wato ‘level 300’ a sashen nazarin Kimiyya da Fasahar Abinci na jami’ar wadda aka tsinci gawarta bayan ta koma ɗakinta.

An ce ɗalibar ta rubuta jarrabawarta ta farko a zangon karatun na farko da ake yi a jami’ar.

Wasu daga cikin abokan karatunta sun danganta mutuwarta da shiga cikin matsi da damuwa a dalilin karatu da kuma zana jarrabawar.

A cikin wasiƙar ta’aziyyar, hukumar jami’ar ta bayyana matuƙar baƙin cikinta dangane da rasuwar Aisha Yahaya.

KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar wani mutum a kan titi a Kano

Sanarwar ta ce, “Aisha ɗaliba ce mai hazaƙa wadda ta rasu a dalilin bugun zuciya. Za a riƙa tunawa da ita a kan sha’awarta na karatu da jajircewarta kan harkokin karatunta.”

Jami’ar ta ƙara da cewa, ba a iya gano wata da ke tattare da ita ba gabanin mutuwarta saboda ba ta nuna alamun rashin lafiya ko fama da wata cuta ba.

Continue Reading

Al'ajabi

Tabar kolarado ta kashe budurwa a Anambara

Published

on

Wata budurwar ta mutu bayan ta yi wa tabar kolarado shan Allah tsine uwar mai ƙarya.

Budurwar, wadda har yanzu ba a bayyana sunanta ba ta mutu bayan shan tabar ce a karshen mako a Awka, babban birnin jihar Anambra.

Wani bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna gawar budurwa a yashe a gefen titi.

Shaidu da ke tare da ita lokacin da abin ya faru sun bayyana cewa da farko bayan ta sha tabar ta suma.

A dalilin haka jama’a suka ba ta garin rogo da yawa ta sha ta farfaɗo, daga bisani ta ƙara zuwa ta sha tabar.

KU KUMA KARANTA: Rikici a kan tabar wiwi ya yi ajalin mutum ɗaya a Gombe

Sha tabar da ta kara yi ne ya birkita ta, inda har ta riƙa tuɓe kayanta tana watsarwa, mutane suka riƙa bin ta suna rufe mata tsiraici kafin daga bisani ta kwanta ta ce ga garinku nan.

Da aka tuntubi kwamandan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Anambra, Daniel Onyishi, ya bayyana irin wannan lamari a matsayin daya daga cikin manyan illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma yadda suke halaka matasa.

A cewarsa, tabar kolorado na da hatsarin gaske ga lafiyar al’umma, da suke lalata rayuwa, su mayar da mutum mara amfani a cikin al’umma.

Ya bayyana cewa ‘kolorado’  tana zama wani irin bala’i da in mutum bai sha ba, sai ya ji kamar zai mutu.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like