Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana cewa harin bam da sojoji suka kai yankin Tundun Biri a Jihar Kaduna wani lamari ne mai firgirtarwa kuma dole a ɗauki mataki.
Ƙungiyar ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin da ya yi sanadin salwantar rayukan masu taron Maulidi sama da 85.
Daraktan Yaɗa Labarai na NEF, Malam Abdul-Azeez Suleiman, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce dattawan sun buƙaci Gwamnatin Jihar Kaduna ta tashi tsaye wajen gudanar da bincike tare da tabbatar da an biya diyya ga waɗanda lamarin ya shafa.
“Baicin biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa, cikakken bincike yana da matukar muhimmanci don tabbatar da adalci, tare da hana aukuwar irin haka a nan gaba, da kuma kiyaye ka’idojin kare hakkin bil Adama da dokokin jin-kai na ƙasa da ƙasa.
KU KUMA KARANTA: Sheikh Muhajjadina ya yi Allah wadai da harin sojoji kan masu Mauludi a Kaduna
“Ta hanyar gano musabbabin faruwar lamarin da kuma yanayin da ke tattare da lamarin, binciken zai iya tantance ko wane irin sakaci ne ya faru, tare da hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.
“Wannan zai samar da diyya, tare da ƙarfafa amincewa tsakanin sojoji da farar hula,” in ji Suleiman.
Ya ce gudanar da cikakken bincike kan harin bam ɗin na da matuƙar muhimmanci don hana aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.
“Waɗannan matakan za su rage hatsarin tashin bama-bamai da kuma kare rayukan fararen hula yayin ayyukan soji. Bincike ya yi daidai da ka’idodin ’yancin ɗan Adam da dokokin jin-kai na duniya.
“NEF na jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna bisa wannan mummunan lamari,” in ji Suleiman.