Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya koma gida Daura a jihar Katsina bayan ya shafe shekaru takwas yana shugabancin Najeriya.
Buhari, da matarsa Aisha da ‘ya’yansa, sun isa filin jirgin Umaru Musa Yar’adua ta jirgin saman sojojin saman Najeriya da misalin ƙarfe 1:30 na ranar litinin.
Ya samu rakiyar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, na sadarwa da tattalin arziƙi na zamani, Farfesa Isa Pantami, da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, da dai sauransu.
KU KUMA KARANTA: Tsohon shugaban ƙasa Buhari ya bar dandalin Eagle Square zuwa Daura
Tsohon shugaban ƙasar ya samu tarba daga sabon gwamnan jihar Katsina Dikko Umar-Raɗɗa da mataimakinsa Faruƙ Lawal.
Daga bisani an kai Buhari Daura a cikin jirgin sama mai saukar ungulu da misalin ƙarfe 2:20 na ranar litinin inda ya samu tarba daga ɗaruruwan jama’a da suka taru a ƙarƙashin jagorancin Sarkin Daura, Umar Faruk-Umar.
Majalisar Masarautar Daura za ta gudanar da gagarumin taron a ranar Talata domin tarbar Buhari da ya dawo gida.