Tsohon shugaban ya ce ya yi abin da zai iya kuma ya bar ’yan Najeriya su yi alkalanci.
Alfijir Labarai ta rawaito tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya ce ba don rufe iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar da aka yi ba, da tuni ya bar Najeriya ya san inda dare ya yi masa.
A hirarsa ta farko tun bayan sauƙarsa daga mulki, Buhari ya shaida wa gidan talabijin na ƙasa (NTA), cewa duk da cewa ba shi ba ne sugaban ƙasa ba, har yanzu mutane ba su bar shi ya huta ba, inda kullum suke zuwa suna takura masa.
Buhari wanda ya miƙa mulki ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu Mulki a ranar 29 ga watan Mayu, ya ce ya yi iya ƙoƙarinsa a cikin a mulkin da ya yi.
Ya ƙara da cewa ’yan ƙasar suna da wuyar sha’ani wanda hakan ya sa shugabantar su ke da wahalar gaske, amma duk da haka, ya yi iya ƙoƙarinsa.
“Allah ya ba ni damar yi wa ƙasata hidima, kuma na yi iya ƙoƙarina. Amma ko abin da na yi ya wadatar, wannan kuma na bar mutane su yi hukunci.
KU KUMA KARANTA: Tinubu ya dakatar da buɗe jami’o’i 37 da Buhari ya amince da kafa su
“’Yan Najeriya suna da matukar wuyar sha’ani. Mutane sun san abin da ya kamata su aikata, amma sai su ƙi, saboda suna ganin sun fi wanda ke shugabantar su sanin abin da ya dace.
“Sun san hakkokinsu kuma suna ganin su suka fi dacewa da kujerar ba wanda ke kai ba, don haka, suna sanya ido a kan duk abin da kake yi.
“Saboda haka kai kuma kullun ƙoƙarinka shi ne gwagwarmaya ba dare ba rana don ganin ka yi yadda suke so,” in ji shi.
Da aka tambaye shi game da nagartar muƙarraban gwamnatinsa ta shekara takwas, Buhari ya mayar da martani da cewa “wannan matsalarsu ce.”.
Ya ƙara da cewa ya kamata masu sukar gwamnatinsa su yi wa kansu tambaya kan rawar da kowannensu ya taka a wajen yaƙar cin hanci da rashawa.
Buhari ya bayyana cewa ya naɗa mutane kuma ya ba su damar gudanar da ayyukansu a lokacin da ya ba su ayyuka, yana mai jaddada cewa idan da za a sake ba shi dama, ba zai yi wani abu daban ba a tsarin Najeriya a yanzu.
Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa ya amince da sauya fasalin takardun naira ne don kare mutuncinsa da kuma tabbatar wa ’yan ƙasa cewa babu ɓarauniyar hanyar da mutum zai bi domin kaiwa ga nasara a zaɓe.
“Ko ’yan Najeriya sun yarda ko ba su yarda ba, mu ƙasa ce da ba ta ci gaba ba. Kuma a irin wannan yanayi, akwai waɗanda ba su damu da yadda suka tara kuɗi ba.
“Har yanzu ina jin cewa hanya ɗaya tilo da zan iya hana waɗannan mutane ita ce kawai in tabbatar da nagartata… Ina ganin a matsayin ƙasa mai tasowa har yanzu muna da sauran aiki a gabanmu.
“Dalilin da ya sa shi ne don nuna wa ’yan Najeriya cewar babu wata ɓarauniyar hanyar da za a bi wajen samun nasarar jagoranci,” in ji shi.