Connect with us

Labarai

Dalilin soke bizar ‘yan Najeriya bayan isar su Saudiyya

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun ce sun fara bincike kan takamaiman dalilan da suka janyo soke bizar wasu gomman ‘yan ƙasar bayan sun sauka a Saudiyya ranar Lahadi.

Fasinjojin 264 waɗanda akasarinsu suka fito daga Legas da Abuja, sun isa filin jirgin sama na King Abdulaziz da ke Jidda a jirgin Air Peace, amma sai Saudiyya suka soke bizarsu, kuma nan take suka nemi a mayar da su gida.

Shugaban ƙungiyar kamfanoni da ke shirya aikin Hajji da Umara a Najeriya, Yahya Suleiman, ya faɗa wa BBC cewa mutanen sun je Saudiyya ne domin halartar taron kasuwanci tsakanin Saudiyya da ƙasashen Afirka, wanda aka gudanar a makon jiya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce tana so ta gano ko matsalar da aka samu ta shafi ofishin jakadanci ne, ko kuma wasu dokoki aka karya da suka shafi sufurin jiragen sama.

Ita ma ƙungiyar kamfanonin shirya aikin Hajji da Umara ta Najeriyar ta ce ta fara nata bincike kan lamarin.

Al’amarin ya faru ne jim kaɗan bayan Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da shugabanni da ‘yan kasuwar Saudiyya, har ma da na ƙasashen Larabawa yayin taron da aka yi tsakaninsu da ƙasashen Afirka.

Har yanzu, Najeriya ba ta warware rikicin hana wasu ‘yan ƙasar bizar shiga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ba, duk da sanarwar da gwamnatin Tinubu ta fitar cewa UAE ɗin ta ba da umarnin cire haramcin.

KU KUMA KARANTA: Saudiyya ta soke bizar ’yan Najeriya 264 bayan saukarsu a Jidda

Cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce za ta tabbatar da cewa ta ɗauki matakan da za su kare aukuwar hakan a nan gaba.

Sai dai ba ta yi wani ƙarin haske ba kan bayanan da ta samu kawo yanzu, tana mai cewa sai ta kammala bincike.

Sai dai shugaban ƙungiyar kamfanoni da ke shirya aikin hajji da Umara a Najeriya, Yahya Suleiman, ya ce bincikensu ya nuna cewa mutanen ba aikin Umara suka je yi ba kamar yadda rahotonni suka bayyana tun da farko.

“Ba Umara suka je ba domin ba bizar Umara suka je da ita ba,” in ji shi yana mai cewa, bizar ‘yan yawon buɗe-ido suka je da ita domin halartar taron ‘yan kasuwa da Saudiyya.

“Sun je da bizar ‘yan yawon buɗe-ido ta kasuwanci ne, kuma ba ma a Najeriya ake yin ta ba. A intanet ake yi, da kuma wasu kamfanoni da aka bai wa damar a Saudiyya, waɗanda mu ba mu san su ba.”

Ya ƙara da cewa an soke bizar tasu ne saboda sun isa Saudiyya a makare – bayan an kammala taron.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like