Dalilin da ya sa ‘yansandan Kano suka gayyaci Sheikh Lawan Triumph

0
265
Dalilin da ya sa 'yansandan Kano suka gayyaci Sheikh Lawan Triumph
Sheikh Lawan Triumph

Dalilin da ya sa ‘yansandan Kano suka gayyaci Sheikh Lawan Triumph

A makon da ya gabata ne, Sheikh Lawan Triumph ya yi wani karatu wanda ake zargin yana cin zarafin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) ta hanyar jingina wa Annabin ƙwarƙwata.

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce tana sane da taƙaddamar da ke tattare da irin salon wa’azin Sheikh Lawal Triumph wanda ya janyo sa-in-sa a tsakanin al’ummar jihar ta Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar, ƴansandan sun ce duk da cewa malamin yana da ƴancin faɗin albarkacin bakinsa, to amma “muna da hurumin ganin mun tabbatar da anyi komai bisa doka da oda”

Hakan ne ya sa kwamishinan ƴan sanda na jihar ta Kano ya gayyaci malamin tare da shiga tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar kamar jami’an gwamnati da jagororin addini da na al’umma domin ganin yadda za a daƙile ci gaba da bazuwar irin wannan rikici a nan gaba.

KU KUMA KARANTA: Ya kamata Sarki Aminu Ado Bayero ya haƙura da bukin hawan Sallah – Sheikh Lawan Triumph

Rundunar ta nemi dukkannin ɓangarorin al’umma da su kai zuciya nesa da gujewa faruwar abubuwan da ka iya rura wutar rikicin.

“Yana da matuƙar amfani a girmama fahimta da abin da jama’a suka yi imanin da shi sannan kuma a tabbatar duk abin da mutum zai yi ka da ya ƙetare iyakar shari’a.” In ji rundunar.

Rundunar ta kuma nemi al’ummar jihar da su miƙa duk wani kokensu ga hukumomin da suka kamata maimakon yin abubuwan da za su rura wutar rikicin a kafafen sada zumunta.

Wannan lamari dai ya faro bayan wani karatu da Sheikh Lawal Triumph ya yi, inda a ciki yake nuna cewa kwarkwata ba ƙazanta ba ce ga ƙabilar Larabawa a wani martani ga masu kore ingancin hadisin da yake nuna cewa kwarkwatar ƙazanta ce.

Hakan ne ya sa sa-insa ta ɓalle a kafafen sada zumunta, inda har al’amarin ya kai ga wasu na kiraye-kirayen halatta jinin Lawal triumph bisa tuhumar kalaman ɓatanci.

Leave a Reply