Dalilin da ya sa kamfanin Ɗangote ya rage farashin man fetur
Kamfanin tace man fetur na Ɗangote a Najeriya, ya sanar da rage farashin litar man fetur da Naira 65.
Wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Laraba a shafin X, wcce VOA Hausa ta gani, ta ce yanzu za a rika sayar da litar man fetur akan Naira 825 maimakon Naira 890.
Sanarwar ta kara da cewa sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 27 ga watan Fabrairun 2025.
Kamfanin ya ce ‘yan Najeriya za su iya siyan man fetur man na Dangote a tashoshin MRS Holdings, za a sayar da shi akan N860 kowace lita a Legas, N870 kowace lita a Kudu Maso Yamma, N880 kowace lita a Arewa, N890 kowace lita a Kudu Maso Kudu da Kudu Maso Gabas.
KU KUMA KARANTA:Ɗangote ya sake rage farashin litar man fetur
Ya kara da cewa wannan man fetur zai kasance a tashoshin AP (Ardova Petroleum) da Heyden akan, N865 kowace lita a Legas, N875 kowace lita a Kudu Maso Yamma, N885 kowace lita a Arewa, N895 kowace lita a Kudu Maso Kudu da Kudu Maso Gabas.
“Wannan muhimmin ragi da muka yi, an tsara shi ne don ya samarwa da ‘yan Najeriya sauki yayin da aka tunkari azumin watan Ramadana.
“Kazalika matakin, nuna goyon baya ne ga shirin farfardo da tattalin arziki kasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake yi.” Sanarwar ta ce.
Wannan shi ne karo na biyu cikin watan Fabrairun 2025 da kamfanin ya rage farashinsa, bayan wani ragi da ya yi na Naira 60 a farkon watan.
Farashin litar man fetur ya yi tashin goron zabi tun bayan da gwamnatin Tinubu ta janye tallafin man fetur da gwamnati ke samarwa kasar, lamarin da ya sa farashin kayayyaki suka cilla sama.