‘Dalilin da muka lakaɗa wa Alkali duka a Gombe’

0
206

Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta kama wasu mutum shida ’yan gida ɗaya da ake zargin su da yi wa alkalin wata babbar kotu dukan kawo wuƙa.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mahdi Mu’azu Abubakar, ya bayyana cewa ana shigar da ƙarar waɗanda ake zargin ne a gaban kotun alkalin da suka lakada wa duka, kan shari’ar filin gona.

A cewar sanarwar, ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙarar ne ya jagoranci ’yan uwansa suka kai wa alkalin da ma’aikatansa duka a lokacin da suka je duba gonar da ake shari’ar a kanta a garin Potuki da ke yankin Degri ba ƙaramar hukumar Balanga.

Yayin zantawa da Aminiya, ɗaya daga cikinsu ya bayyana cewa suna cikin gona suna aiki ne kawai suka ga mutane sama da 30 suna zagaya gonar, kuma ba su san kowa a cikinsu ba, sai ’ya’yan kawunsu biyu da suke shari’ar gonar da su, kuma kotu ba ta faɗa musu cewa za a zo duba gonar ba.

KU KUMA KARANTA: An yi wa Alkali dukan kawo wuka a Gombe

Abubakar Umaru, ya ce ganin mutanen da yawa da waɗannan ’yan uwan nasu da suke rikicin gonar da su, ta sa zuciya ta ɗebe su suka kai musu hari suka ji musu ciwo ba tare da sanin akwai alkali a cikinsu ba.

“Mun saba ganin mutane suna zuwa gonarmu haka suna dubawa daga ƙarshe kawai sai mu ji an sayar, ba yadda muka iya, shi ya sa a wannan karon ba mu bari ba, muka tarwatsa su” in ji shi.

A cewarsa, daga baya ne suka gane akwai alkali a cikin mutanen, wanda hakan ya sa suka yi nadamar abin da suka aikata.

Abubakar, ya roƙi alkalin da sauran da mutanen da su yafe musu kuskuren da suka yi.

“Wannan shari’ar gadar ta muka yi, domin daga rasuwar mahaifinmu ko addu’ar kwana uku ba a yi ba waɗannan ’yan uwa namu suka kawo mana sammaci a kan cewa mun gaji shari’ar da suke yi da mahaifinmu kan gonar gado tun da shi ya rasu,” in ji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar 4 ga watan Nuwamba 2023 ne mutanen suka yi wa alkalin babbar kotu ta da ke garin Gombe dukan kawo wuka.

Leave a Reply