No menu items!

Sample Page Title

Date:

Dakarun sojin Mali sun kashe ɗaya daga manyan kwamandojin ƴan ta’adda a yankin Sahel, kamar yadda rundunar sojin ƙasar ta sanar a ranar Talata.

An kashe Abu Huzeifa, wanda ake ƙira da Higgo a safiyar Lahadin da ta wuce a wani samame da aka kai yankin Menaka da ke arewacin ƙasar, kusa da iyaka da Nijar, a cewar sanarwar rundunar sojin.

Ya yi aiki a matsayin kwamandan sojin ƙungiyar ƴan ta’adda ta Daesh/ISIS a yankin iyakokin ƙasashen Sahel, Mali da Nijar da kuma Burkina Faso.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan Houthi sun yi iƙirarin kai hari kan jiragen ruwa 4, ciki har da na Amurka 2

Rahottanin sun bayyana cewa Huzeifa na da hannu a wani mumunar hari da aka kai a shekarar 2017 kusa da ƙauyen Tongo Tongo a Jamhuriyar Nijar inda aka kashe dakarun sojin Amurka na musamman guda huɗu da na Nijar huɗu.

A sakamakon hakan ne Amurka ta saka tukuicin da ya kai dala miliyan 5 ga duk wanda ya samo mata shi ko yake da labarin inda yake.

Rundunar ta ce Huzeifa dan kasar waje ne, wasu rahotanni sun bayyana yiwuwarsa na zama ɗan asalin Jamhuriyar Sahrawi ne.

Rahotani sun ce ƙungiyar Huzeifa ta yi fice da kai hare-hare a yankin Menaka na kasar Mali, inda ake yawan zarginta da kai hari kan ƴan kasar ta Mali.

Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar ne suke da mafi yawan mace-macen mutane sakamakon ayyunkan ta’addanci a yankin, a cewar ƙididdigar rahoton ‘Global Terrorism Index 2024’ da Cibiyar Tattalin Arziki da Zaman Lafiya ta Australia ta fitar.

Kasashen uku dai na fuskantar matsalar tabarbarewar tsaro, inda ƙungiyoyin da ke da alaƙa da al-Qaeda da Daesh/ISIS ke kaura daga ƙasar Mali zuwa yankuna makwabta da ke yankin na Sahel.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...