Dakarun MƊD sun kammala ficewa daga Mopti dake ƙasar Mali

0
149

Dakarun Majalisar dinkin duniya a jiya juma’a sun miƙa ɗaya daga cikin sansanoninsu ga hukumomin Mali, a ci gaba da shirin da suke yi na ficewa daga ƙasar baƙi ɗaya.

Mai magana da yawun dakarun, Fatoumata Kaba tace an miƙa sansanin dakarun majalisar ne dake garin Mopti, ɗaya daga cikin ‘yankunan da yayi fama da matsalar ‘yan ta’adda da masu iƙirarin jihadi.

Kaba tace an gudanar da miƙa sansanin cikin kwanciyar hankali, saɓanin abinda aka gani a baya, wanda ya kaiga arangama tsakanin sojojin Mali da ‘yan ta’adda.

KU KUMA KARANTA: Ghana na karɓar baƙuncin taron MƊD kan aikin sojojin wanzar da zaman lafiya

Sansanin sojin Mopti na ɗauke da dakarun da suka fito daga ƙasashen Bangladesh da Togo, waɗanda suka karɓi aiki daga sojojin Masar da Pakistan da Senegal.

Ana saran dakarun majalisar da ake ƙira MINUSMA su kammala ficewa daga Mali nan da ranar 31 ga watan nan na Disamba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here