Dakarun Isra’ila sun kutsa kudancin Gaza, ƙungiyoyin bayar da agaji sun yi gargaɗi

0
160

Dakarun Isra’ila sun kutsa kudancin Gaza, inda dubban fararen-hula suka tsere domin neman mafaka daga luguden wutar Isra’ila da kuma gumurzu tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas mai fafatukar kare hakkin Falasɗinawa.

Ƙungiyoyin bayar da agaji sun yi kakkausan gargaɗi game da “matsalar rashin jinkai” da ake fama da ita a Falasɗinu, suna masu cewa yankin yana dab da faɗawa cikin yunwa da cututtuka.

Hamas ta ce Isra’ila ta ƙaddamar da jerin “manyan hare-hare” a Khan Younis da kuma hanyar da ta haɗa birnin da Mashigar Rafah, a kusa da kan iyaka da Masar.

Wani wakilin AFP ya bayar da labari kan luguden wutar ya mamaye kudancin Gaza da sanyin safiyar Lahadi.

Leave a Reply