Daga ƙarshe Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya taya zabaɓɓen gwamnan jihar, Engr. Abba Kabiru Yusuf murnar nasarar da yayi na lashe zaɓen gwamnan jihar.

Rahotanni sun nuna cewa Gawuna a cikin saƙon mintuna biyu da daƙiƙa goma sha biyar na sautin murya da ya naɗa a ranar laraba, ya yi addu’ar Allah ya yi wa zaɓaɓɓen gwamna jagora.

Ya kuma buƙaci magoya bayansa da su yi haƙuri su kwantar da hankalinsu duk da cewa sun kai ƙara ga INEC suna buƙatar a sake duba sakamakon zaɓen gwamna amma alƙalan zaɓen bai amince da hakan ba.

KU KUMA KARANTA: Ba zan saka Matana da ‘Ya’yana cikin Gwamnati ba – Abba Gida Gida

“Mun riga mun gabatar da kokenmu kan batutuwan da suka faru a lokacin zaɓen gwamna da suka sanya sakamakon zaɓen ya gaza, don haka ne muka buƙaci a sake nazari domin a gudanar da zaɓen a wuraren da aka gano kura-kurai, saɓanin yadda INEC ta bayyana ɗan takarar da ya yi nasara a zaɓen gwamna.”

“Amma a yau, 29 ga Maris, 2023, INEC ta sake tabbatar da wanda ya lashe zaɓen gwamna, tare da ba ɗan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Kabiru Yusuf takardar shaidar cin zaɓe, ina so in tunatar da jama’a cewa kafin wannan lokaci , mun roƙi Allah ya ba mu nasara idan har hakan zai kasance maslaha ga kowa da kowa, idan kuma akasin haka, Allah Ta’ala ya yi mafificin alheri.”

Gawuna ya yi ƙira ga magoya bayansa da su yarda da imani kuma su jajirce wajen neman yardar Allah. ‘’Ina matukar godiya ga magoya bayanmu da masu yi mana fatan alheri da suka fito domin kada kuri’a a zaɓen gwamna da aka yi a ranar 18 ga Maris.’’

‘’Ina rokon Allah Ya yi wa gwamnan da aka zaɓa jagora, domin ya sami ikon yi wa kowa adalci, mu kuma mu kasance masu bin doka da oda’’.

Tun da fari dai zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a ya karɓi takardar shaidar cin zaɓe daga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa a ranar laraba

Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023 bayan ya doke abokin hamayyarsa kuma dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna.

A cewar jami’in zaɓen gwamnan jihar, Farfesa Ahmed Doko Ibrahim, Abba Kabiru Yusuf ya lashe zaɓen da ƙuri’u 1,019,602 inda ya doke Gawuna na APC wanda ya samu ƙuri’u 890,705.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *